Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

31 Disamba 2023

10:32:39
1425352

Anyi Musayar Wuta Tsakanin Jiragen Saman Amurka Da Jiragen Ruwan Yaman

Jiragen saman Amurka masu saukar ungulu sun yi musayar wuta da jiragen ruwan Yaman a tekun Bahar Maliya

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Babban kwamandan rundunar sojin Amurka da ke yammacin Asiya, mai suna CENTCOM, ya mayar da martani kan lamarin da ya auku a kusa da tashar jiragen ruwa ta Hodeidah ta kasar Yaman, inda ya fitar da sanarwa da cewa, jiragen ruwan 'yan Houthi na Yaman sun kai hari kan wani jirgin ruwan kwantena da jirage masu saukar ungulu na sojojin ruwan Amurka a yankin kudancin Bahar Maliya.

A cikin wannan sanarwar, Centcom ta ce wani jirgin ruwan kwantena na kamfanin jigilar kayayyaki na "Maersk" ya yi kiran gaggawa sau biyu cewa jiragen ruwa 4 na 'yan Houthi na Yaman ne suka kai masa hari.