Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

30 Disamba 2023

19:46:35
1425229

Yadda Taron Ganawa Na Wakilan Majalisar Koli Ta Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Da Shugabannin Lardin Quds Razawi Ya Gudana + Hotuna

Gungun mambobin majalisar koli ta majalisar Ahlul-Baiti (AS) ta duniya sun gana da Hujjatul Islam wal-Muslimin Ahmad Marawi.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa, mambobin majalisar koli ta majalisar Ahlul-Baiti (AS) ta duniya sun gana da Hujjatul Islam wal-Muslimin Ahmad Marawi, wanda shine shugaban Ustan Quds Razawi, a yammacin Alhamis - 28 ga December 2023.

A cikin wannan taron ganawar da ya gudana a dakin taro na haramin Imam Rida (a.s) da wasu gungun mambobin majalisar koli ta majalisar duniya ta Ahlul Baiti (a.s) sun halarta tare da daga cikin mataimaka da manajoji na wannan majalisa.

A farkon wannan taro, Ayatullah Riza Ramazani, babban Shugaban majalisar duniya ta Ahlul-Bait (AS) ya bayyana manufa da hadai na wannan majalissar, kuma yayi bayanin gudanar da taron majalisar koli ta wannan majalisa karo na 193.

Ayatullah Ramezani ya yi la'akari da mafi girman manufa da hadafi na Majalisar Ahlul-baiti (a.s) a matsayin karfafawa 'yan Shi'a da magoya bayan Ahlul Baiti (a.s) ya ce: babban taron majalisar Ahlul Baiti (a.s) na duniya ana gudanar da shi ne sau daya a shekara, haka nan kuma a cikin shawon shekarar ma ana gudanar da taron na musamman na zabbabbu bisa dacewa da wasu lamurra na gaggawa da suka auku. A taron da za a yi a ranakun 7 da 8 ga watan Day shekara ta 1402 a birnin Mashhad, baya ga tattaunawa ta musamman dangane da ayyuka da batutuwa da kuma rahotanni kan ayyukan da wakilai da sassa daban-daban na majalissar suka gabatar, kowanne daga cikin 'yan majalisar koli, wadanda suka fito daga kasashe daban-daban kamar Iraki, Labanon, Iran, Siriya, Kuwait da wasu kasashe suna bayyana halin da 'yan Shi'a ke ciki a sassa daban-daban na duniya.

Babban magatakardar majalisar dinkin duniya ta Ahlul-baiti (AS) ya kara da cewa: burin manbobin majalisar koli na majalisar shi ne cewa majalisar Ahlul-baiti (AS) ta kai matsayi madogara ta ilimi da ruhiyya. Domin musulmi da wadanda ba musulmi ba su koma domin koyi da kuma amfana da koyarwar Ahlul Baiti (AS).

Ayatullah Ramezani yayin da yake ishara da irin nasarorin da Majalisar Ahlul Bayt As ta cimma a cikin shekara guda da ta gabata ya ce: A bisa manufofin majalisar, baya ga ayyuka da batutuwa daban-daban a cikin matakai daban-daban, an tarjama da buga litattafai dubu biyu a cikin harsuna 58. Sanna akwai kafar Wiki Shi'a a matsayin kundin ilimi, ga kuma kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Bait (AS) - ABNA - mai watsa labaran Shi'a da cibiyoyin Shi'a na duniya da koyarwar Ahlul-Baiti (AS) a cikin harsuna 27, du kansu suna  daga cikin ayyukan Majalisar Ahlul Bayt As.

Ayatullah Ramezani ya jaddada dabarun da mambobin majalisar koli suke bi wajen karfafa shirye-shirye da ayyuka ya kara da cewa: Wannan wata dama ce ta zinari, kuma ba a taba samun wani yanayi na dama domin yada da ci gaban mazhabar Ahlulbaiti (AS) ba. ) kamar a wannan lokacin ba, kuma fasahar Majalisar Ahlul Bayt As ita ce Nazariyyar Ahlul Baiti (a.s) da Nazarin juyin juya halin Musulunci su kasance a karkashin bahasin hankali da ruhiyya da adalci.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da abubuwan da suke faruwa a wannan yanki da ma duniya baki daya, babban sakataren majalisar Ahlulbaiti (AS) ya ce: farin jini da kuma kula da mazhabar Ahlulbaiti (AS) ya karu matuka bayan juyin juya halin Musulunci. kuma hakika bayan juyin juya halin Musulunci, al'ummar duniya sun kara karkata zuwa ga Musulunci, amma abin da ya faru a Palastinu da Gaza a baya-bayan nan ya tabbatar wa duniya hakikanin Musulunci fiye da da.


Mamber a majalisar koli ta majalisar Ahlul-baiti (AS) ta duniya ya ci gaba da cewa: A yau idan muna son yin nazari a kan Gaza da Palastinu to da farko zamu mu kasa batun zuwa kashi biyu kafin guguwar Al-Aqsa da kuma bayan guguwar Aqsa. Dukkan laifuffukan ta’addancin da suka faru a Palastinu a cikin wadannan shekaru, an sanya su ne a bangare guda, sannan a daya bangaren kuma laifukan ta’addanci da aka yi a watannin baya. Bugu da kari, abubuwan da suka faru a Gaza na baya-bayan nan sun fallasa irin munafuncin da wasu kasashe ke da'awar kare hakkin bil'adama.

Ayatullah Ramezani ya ci gaba da cewa, cikin yardar Allah da jagoranci da kuma hikima ta Ayatullahi Imam Khamene'i da irin ayyukan gwagwarmaya da kuma dattijai irin su Sayyid Hasan Nasrallah da sauran masoya a wannan fage muna shaida irin yunkuri da ci gaban da Shi'a ta samu a duniya. Musamman karktowar wadanda ba musulmi ba zuwa ga Musulunci da mazhabar Ahlul Baiti (AS) ya karu bayan waki'ar Gaza.

Babban sakataren majalisar duniya ta Ahlul Baiti (AS) ya ci gaba da cewa: A tarukan majalisar koli ta majalisar dangane da karfafa bangaren al'adu, an kuma tattauna batutuwa tare da musayar ra'ayi ta yadda lamarin zai kasance wajen shiryatar tare da jagorantar ‘yan Shi’a ta fuskancin hankali da hikima.

A karshen jawabin nasa ya ce: Idan har makaranta da koyarwar Ahlul-Baiti (A.S) suka fadada kuma suka inganta, to za mu kasance masu nasara a fagen, kuma gwargwadon yadda ayyukan da suka shafi hakan suke kara zurfafawa sa'a da maraba da karbuwa za su samu.

A cikin wannan taro, Ayatullah Muhammad Hassan Akhtari, shugaban majalisar koli ta majalisar duniya ta Ahlul-Baiti (a.s), yayin da yake ishara da gudanar da wannan taro a kusa da hubbaren Sayyidina Imam Ali bin Musa Arri-Ridha, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da kuma batutuwa na musamman da aka gabatar a wannan taro, ya ce: Akwai bukatar Majalisar Ahlul-Baiti (a.s) Ta Duniya da Ustan Quds Razawi su aiwatar da hadin kai da hadin gwiwa mai inganci a fagen bincike da nazari.

Hujjatul Islam Sayyid Ammar Hakim, yayin da yake bayyana jin dadinsa da halartar taron Majalisar Ahlul-baiti (AS) Ta Duniya da kuma ganawarsa da shugabannin Lardin Al-Quds Razawi, yayin da yake ishara da irin karfin da kasar Iraki ke da shi, ya ce: Wannan kasa saboda samuwar gurarae masu tsarki da kuma Hauza Ilmiyyah tana da rawar da ta taka ta musamman wajen samuwar 'yan Shi'a da ta wanzu a lokuta daban-daban kuma Iran da Iraki za su iya taka muhimmiyar rawa a fagen al'adu da inganta al'adun Shi'a a duniya. A cikin makonni da watannin da suka gabata ne kasar Iraki ta fito fili kan batun Gaza da kuma zaluncin da gwamnatin sahyoniyawan ta ke yi wa al'ummar Palastinu da ake zalunta, haka nan kuma kungiyoyin gwagwarmaya na Iraki sun yi matukar taka rawa.

Hujjatul Islam wal-Muslimeen Marwi shugaban lardin Quds Razawi a lokacin da yake maraba da majalisar koli ta majalisar Ahlul Baiti (a.s.) ta duniya da wakilai da jami'an wannan majalissar ya ce: Ina jin farin ciki da samun daukakr kasancewa a cikin rukuninku, masu alfahari da kasancewarsu Ahlul Baiti (a.s.). Majalisar Ahlul Bayt As Ta Duniya saboda jinginuwarta da mazhabar Ahlul Baiti (AS) ta zamo abin kauna da abin so, kuma mu samu gwargwadon hidima ga wannan rukuni mai matukar girma, muna ganin ya zama wajibi a garemu mu ci gaba da bunkasarta da fadada ta.

Yayin da yake ishara da hadisin haske na Sayyidina Ali Ibn Musa al-Reza (a.s.) dangane da raya da Ahlul Baiti (a.s.) da yada karantarwa da fa'idar maganganun wadannan ma'abota daraja, ya ce: Wannan magana mai albarka tana iya kasancewa ita ce hikimar samuwar Majalisar Ahlul Baiti (a.s.) ta duniya.

Hujjatul Islam wal-Muslimin Marawi ya dauki samar da kungiyoyi biyu masu daraja, Majalisar Ahlul-Baiti (a.s) Ta Duniya da Majalisar kusanci ga mazhabobin Musulunci a matsayin wani shiri da dabara na Jagoran juyin juya halin Musulunci a hangen kasa da kasa, kuma ya ce: Ayatullahi Imam Khamenei ta hnayar kirkirar Majalisar kusanci ga mazhabobin Musulunci ya cusa tare da isar da sakon cewa a cikin Musulunci babu wata iyaka ta kabilanci da ta mazhaba, kuma cewa wannan iyakar kafirci ce, kuma iyakar tazarar da ba ta kai ta kafirci ba kirkirar makiya ce. Falsafar kafa Majalisar Ahlul Baiti (A) ta duniya a haƙiƙa ita ce samar da taska na ilimi da al'adu don samar da kusanci a tsakanin musulmi, wato tare da koyarwar Al-Qur'ani na Manzon Allah (S) da Ahlul Baiti (A.S). A) za mu iya taimakawa wajen kusantar da duniyar Musulunci; Kamar yadda jawabin Imam Riza (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ma yana isar da wannan sako.

Shugaban Ustan Quds Razawi, yayin da yake jaddada cewa majalissar kusanvto da mazhabobi da kuma majalisar Ahlul-Baiti (AS) ta duniya suna da alaka da juna, ya ce: Muna cikin hidimar wadannan majalisosi guda biyu a hubbaren Sayyidina Ali bin Musa Al-Reza (AS). ) don amfani da damar da wadannan majalisosi guda biyu suke da shi wajen saukaka aikin ziyarar maziyarta daga kasashen waje domin mu amfana da shi.

Hujjatul Islam Wal-Muslimin Marawi ya bayyana cewa babu wani daga cikin gwamnatocin da suka maida hankali sosai kan lamarin aikin ziyara domin wannan muhimmin lamari ya kasance a gefe yana mai cewa: Dangane da haka a wata ganawa da na yi da Dr. Amir Abdullahian Mai girma Ministan Harkokin Waje, na ba da shawarar samar da tsari a ma’aikatar harkokin wajen, na tabo batun aikin ziyara, an yi maraba da wannan batu kuma an aiwatar da shi, dangane da hakan muna godiya.

Ya kara da cewa: Watakila a baya an yi watsi da batun kula da ayyukan ziyara da mika shi ga hukuma, amma yanzu yanayin da suka shafi aikin ziyara da na harami mai alfarma ga shugaban kasa, wanda a da ya taba zama hadimi ga wanna harami da ma'aikatar kotu bangaren shari'a sun sha bamban, Kuma muna jin cewa sun dauki hakan a matsayin zama wajibi a wannan bangaren idan kuwa ya zamo daga garesu ne to ba za su gaza ba.

Hujjatul Islam Marawi ya kara da cewa: Gudanarwa da kawar da cikas ga aikin ziyarar ‘yan Shi’a da Majalisar Ahlul-baiti (AS) ta duniya ke yi na iya zama daya daga cikin ayyukan majalisar; Har ila yau, masu ba da shawara kan al'adu da jakadu su ma suna iya yin ƙoƙari sosai a wannan al'amari.

Daga karshe shugaban lardin Quds Razawi, yayin da yake ishara da kasancewar wasu mutane irin su Hujjatul Islam wal Muslimeen Sayyid Ammar Hakim, Hujjatul Islam Sheikh Ibrahim Zakzaky da sauran fitattun mutane daga wasu kasashe, ya ce: Muna ganin ziyarar ku a matsayin alheri da nasarar dacewa a garemu .

...................................