Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

28 Disamba 2023

08:30:47
1424428

Jagora: Malama Zenatudden Alzakzay Tayi Hakuri Kamar Dutse Akan Musibun Da Suka Sameta

Jinjinar Jagoran Juyin Juyi Halin Musulunci Ga Mai Dakin Shaikh Ibrahim Ya'aqub Alzakzay Bayan Gama Jawabinta

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: a wani taron mata da jagoran juyin juya halin Musulunci ya jagoranta ajiya Laraba yayi tsokaci bayan Malama Zenatudden Alzakzay Tayi bayani inda yace: Ina godiya ga mai girma Malama Zeenatuddin mai dakin Sheikh Zakzaky (h) wadda ta yi jawabi anan yanzu, mahaifiyar shahidai shida' ya'yanta uku suka yi shahada a waƙi'a guda, a wata waƙi'ar wasu ukun suka yi shahada, wannan matar tayi hakuri ta kafe kamar dutse, ta zauna a kurkuku na tsawon lokaci, kuma ta jure ma wahalhalu masu yawa.

Wani sashe na jawabin Jagoran Juyin juya halin Muslunci, Imam Khamne'iy (DZ), bayan kammala jawabin Malama Zeenatuddin.

27/12/1445.