Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

25 Disamba 2023

18:05:25
1423600

Cewar Haj Qasim Sayyid Radhi "Kai Ma Ya Kamata Ace Ka Zamo Shahidi!

Shahadar Daya Daga Cikin Mashawartan IRGC A Zainabiyyah, Damascus

An ji karar fashewar wani abu daga yankin Zainabiyah da ke Damascus

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Wasu majiyoyi na cikin gida a kasar Siriya sun rawaito cewa yahudawan sahyoniya sun kai hari a wani wuri da ke kusa da Zainabiya a birnin Damascus.

A ci gaba da farmakin da gwamnatin sahyoniyawan yahudawan sahyuniya suka kai a yankin Zainabiya da ke wajen birnin Damascus sa'o'i da suka gabata, Kwamanda Sayyid Radhi Musawi, wanda aka fi sani da Sayyid Radhi, daya daga cikin manyan mashawartan IRGC a kasar Siriya ya yi shahada.

Sardar Sayyid Redhi Musawi ya kasance daya daga cikin tsofaffin masu ba da shawara ga rundunar Quds Force ta IRGC a Siriya kuma abokin Haj Qassem Suleimani a kasar Siriya, wanda ya kasance mai fafutuka a fagen bayar da goyon baya ga 'yan adawar Siriya.

Cewar Haj Qasim Sayyid Radhi "Kai Ma Ya Kamata Ace Ka Zamo Shahidi!

Tunawa da shahidi Sayyid Radhi Musawi daya daga cikin kwamandojin IRGC a kasar Siriya wanda ya yi shahada a yau sanadiyyar harin gwamnatin sahyoniyawa.

Bayan jin labarin shahadarsa yahudawan sahyoniya suna shirye domin mayar da martani ga yuwuwar ramuwar dakarun IRGC kan kisan da aka yi wa Sayyid Radhi

Jaridar Jerusalem Post ta jami'an yahudawan sahyoniya ita ta nakalto wannan labarin tana mai rubuta cewa Isra'ila na sa ran mayar da martani ga shahadar mai baiwa IRGC shawara a bangaren arewacin kasar.