Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

24 Disamba 2023

06:48:40
1423064

An Kai Harin Ga Jirgin Isra'ila A Kusa Da Tekun Indiya A Daren Jiya

Tashar talabijin ta Hebrew 12 ta fitar da sabbin bayanai kan harin da aka kai kan jirgin ruwan Isra'ila mai dauke da tutar Laberiya a kusa da Indiya.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Tashar talabijin ta Hebrew 12 ta fitar da sabbin bayanai kan harin da aka kai kan jirgin ruwan Isra'ila mai dauke da tutar Laberiya a kusa da Indiya, jirgin da ya kai wa wannan jirgi hari kai tsaye daga kasar Iran ne kuma 'yan Houthi na Yaman ba su suka kai harin ba kamar hare-haren baya; Wannan lamari dai ya faru ne a daren jiya.

Ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta kuma yi ikirarin cewa jirgin ruwan dakon mai mai suna MV Chem Pluto, dauke da tutar kasar Laberiya, Iran ta kai hari inda ta kai masa hari da wasu jiragen yaki mara matuki a nisan mil 200 daga gabar tekun Indiya.