Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

24 Disamba 2023

04:56:29
1423014

Ana Cigaba Da Gudanar Da Zanga-zangar Nuna Goyon Bayan Falasdinu A Sassa Daban-daban Na Turai

Ana Cigaba Da Gudanar Da Zanga-zangar Nuna Goyon Bayan Falasdinu A Sassa Daban-daban Na Turai

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Dubban mutane ne a nahiyar Turai suka fito kan tituna domin nuna goyon bayansu ga Falasdinu.

Kimanin mutane 1,500 ne suka yi tattaki a titunan Berlin, babban birnin kasar Jamus, zuwa kofar Brandenburg tare da neman kawo karshen yakin Gaza.

Masu zanga-zangar a Netherlands sun yi maci a kan tituna tare da tsayawa a gaban kamfanonin kasa da kasa, ciki har da McDonald's da Starbucks, suna rera taken "Shame on you!" suka daddaga tutocin Falasɗinu Suna masu bukaci wadannan kamfanonin sarrafa kayayyakin abinci da su kaurace wa Isra’ila a matsayin martani ga yakin Gaza.

A kasar Sweden itama duk da dusar ƙanƙara da sanyi, dubban masu zanga-zangar sun taru a gaban ofishin jakadancin Isra'ila da ke Stockholm, babban birnin wannan ƙasar. Masu zanga-zangar sun bukaci a mayar wa al'ummar Palasdinu filayen da aka kwace.