Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

21 Disamba 2023

11:19:41
1422179

An Ƙaddamar Da Sabbin Ayyukan Wallafa 110 Na Majalisar Ahlul-Baiti (AS) A Cikin Harsuna 22.

An gudanar da bikin kaddamar da sabbin wallafe-wallafen Majalisar Ahlul-baiti (AS) tare da halartar Ayatullah Ramazani, babban sakataren wannan majalissar.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya kawo maku rahoton cewa: an gudanar da taron bukin kaddamar da sabbin wallafe-wallafe na Majalisar Ahlul-baiti (A.S) ta duniya kafin sallar azahar a yau Alhamis 30 ga Azar 1402 wanda yayi daidai da 21 ga watan Disamba 2023 tare da jawabin Ayatullah Ramazani babban sakataren wannan majalisar da kuma Ayatullah "Dari Najaf Abadi" mataimakin shugaban majalisar koli ta majalisar a ginin majalisar Ahlul-Baiti (AS) da ke birnin Qum.

An Fassarar Littafai 110 A Majalisar Ahlul Baiti (AS) Zuwa Harsuna 22 Na Duniya.

Hujjatul-Islam Walmuslimeen Mehdi Farmanian mataimakin shugaban majalisar duniya ta Ahlul Baiti (As) a fannin kimiya da al'adu na Ahlulbaiti (a.s) a cikin wannan biki, yayin da yake ishara da ayyukan wannan majalissar a fagen fassarar littafai, ya bayyana cewa: Daga cikin Ayyukan Mataimakin Shugaban Kimiyya da Al'adu na Majalisar, shine fassarar mujalladan littattafai 110 zuwa harsuna 22. Wanda Za a bayyana tare da gabatar da waɗannan ayyukan a yau. Manufarmu ita ce, a buga littattafan a cikin ƙasashen da aka yi niyya kuma a shirye muke mu ba da haɗin kai don buga waɗannan littattafai a ƙasashen waje.

Ya ci gaba da cewa: Daga cikin littafan da aka tarjama majalissar Ahlul-baiti (AS) a bana, littafai 18 cikin harshen Turkanci, littafai 11 a Yaren Hausa, littafai 9 cikin harshen faransanci, littafai 9 a cikin yaren Turanci, litattafai 7 a yaren Pashto, litattafai 6 a cikin yaren Indonisiya, littafai 6 cikin harshen Larabci, littafai 5 cikin harshen Swahili, littafai 5 cikin harshen Urdu, littafai 4 cikin harshen Urdu da kuma 4 a Yaren Tajik.

Mataimakin shugaban majalissar Ahlul Baiti (AS) a fannin kimiya da al'adu ya kara da cewa: "Wiki Shi'a" mai suna "Wiki Shi'a" na daga cikin abubuwan karramawa na majalissar ilimi da al'adu ta majalisar Ahlul Baiti (AS) ta duniya, wadanda adadinsu ya kai Harsuna 22 kuma suna samun masu ziyaratarsu miliyan 14 a kowane wata. A wannan shekara, an ƙara mashiga 6,000 zuwa Wiki ta Shi'a, kuma adadin waɗannan mashigar zai kai 8,000 a ƙarshen shekara, kuma yanzu akwai mashigar kafa 32,000 a cikin harsuna 22 a cikin Wikin Shi'a.

Majalisar Ahlul-baiti (AS) Ta Duniya A Kan Tafarkin Samun Madogarar Ilimi 

Ayatullah Reza Ramezani, babban sakataren majalisar ta Ahlul-Baiti (AS) ya yi ishara da sharuddan da suka wajaba wajen gudanar da bincike ya kuma bayyana cewa: Wajibi ne a mai da hankali kan abubuwan da ake bukata na duniya da na lahira, sannan samar da ilimi wanda ya kasance mai tushe akan halayya. Domin duk wani bincike da ake son ya samar 'ya'yan anfani dole ne a yi haƙuri akansa kuma ba wai kawai zai kasance mai saurin samuwa ba ne, sai dai shi bincike yana da jinkirin tabbatuwa wajen cin Nasararsa Ya kamata a sami daidaituwa tsakanin cibiyoyin bincike kuma ana samun haɗin kai bayan gane fahimta da hulɗa.

Ya jaddada: Idan ilimi bai kasance tare da kyakkyawan ɗabi'ar halayya da ruhiyya ba, ba zai zama na hankali ba kuma ba za a iya sarrafa shi ba. Don haka dole ne ilimi ya kasance karkashin ikon takawa, wannan magana ta shafi ko da ilimin tauhidi da ilimin halayya ne. Idan har al'umma ta kasance a kan tafarkin ilimi to ita ce jagora, kuma a wannan al'amari ya kamata Majalisar Ahlul-baiti (AS) ta samu karfin ilimi da ruhiyya, kuma mun yi nesa da wannan manufa.

Babban Shugaban majalisar Ahlul Baiti (A.S) ta Duniya ya kara da cewa: Wajibi ne mu gabatar da tushen koyarwar Ahlul Baiti (A.S) ba ga mutane daidaiku kadai ba, har ma da manyan masu matsayi duniya, idan ya zamo mun gabatar da Ahlul Baiti As kamar yadda ya dace to ko shakka babu mutanen zamani mu zasu bi wannan tafarkiin tunanin. A yau, muna fuskantar ra’ayoyi masu karo da juna, kuma ra’ayin da ya mai da hankali ga sha’awoyi da hakika, to tabbas zai zama maganin matsalolin ’yan Adam.

Akwai Damarmaki Da Yawa A Duniya Don Gabatar Da Koyarwar Makarantar Ahlul Baiti As

Har ila yau, Ayatullah Qurban Ali Dari Najaf Abadi ya ce a cikin wannan biki: jagoran juyin juya halin Musulunci Bayan fara jagorancinsa ya kafa cibiyoyi guda biyu, Majalisar Ahlul Baiti (AS) ta duniya da kuma majalisar kusantar juna ta mazhabobin addinin Musulunci. wanda shi ke nuna shi misali ne sanin damarmaki. A yau aikin kungiyoyin gwagwarmayar Palastinawa na daya daga cikin damarmaki da juyin juya halin Musulunci na Iran ya haifar, juyin juya halin Musulunci na Iran ya kasance wani yunkuri ne na samar da damarmaki.

Ya ci gaba da cewa: A yau, an samu sabbin damammaki na gabatar da fuskar Musuluncin Muhammady sahihi kuma tsantsa, bisa ga abin da ke cikin littattafanmu da bincikenmu, ya kamata mu yi kokarin sanin ilimin Musulunci da isar da shi ga duniya da kare hakikanin Musulunci. Dangane da haka Imam Khumaini (r.a) ya bar mana amana mai girma a kawukanmu.

Mataimakin Shugaban Majalisar koli ta Majalisar Ahlul Baiti (AS) ya kara da cewa: Wajibi ne mu yi iya kokarinmu wajen kare mazhabar Ahlul Baiti (AS) wacce ita ce mazhabar bil'adama. wadanda suke a Majalisar Ahlul-baiti (AS) da sauran kasashen duniya, duniya na bayar da hadin kai ga wannan dandalin, suna yin gagarumin aiki. Tun farkon kafuwar majalissar manya manyan mutane irin su Ayatullah Asefi, Shahid Ayatullah Hakim, Ayatullah Taskhiri. Wanda ni na samu damar yin aikin soja kafin kafa Majalisar Ahlul Baiti (AS) ta duniya. Ya kamata kowa ya taimaka wajen ganin an samu gagarumin sauyi a wannan dandalin a fagage daban-daban, musamman hanyoyin sadarwa.

A bangare na karshe na bikin, an karrama gungun manyan masu fassara da masu fafutukar al’adu daga kasashe daban-daban da takardar shaidar yabo da kyaututtuka.

A bangare na karshe na bikin, tare da halartar Ayatullah Ramezani, babban sakataren majalisar Ahlul Baiti (AS) ta duniya, Ayatullah Dari Najafabadi, mataimakin shugaban majalisar koli ta majalisar Ahlul Baiti (AS), da kuma Hujjatul-Islam Walmuslimeen Alami Balkhi Shugaban Majalisar Masoya Ahlul Baiti (AS) na kasar Afganistan an gabatar da littafai 110 da aka fassara zuwa harsuna 22 na duniya da kuma littafai na sauti guda biyar da aka karantasu cikin Audio.