Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

19 Disamba 2023

04:55:33
1421414

Tarukan Ta'aziyyar Gida Yana Ƙara Dankon Zumunci Tsakanin Iyalai

Babban magatakardar majalisar dinkin duniya ta Ahlul-baiti (A.S) ya yi nuni da cewa dangane da wajabcin gudanar da tarukan gidaje na jajantawa da ake gudanarwa ya ce: Tarukan majalisan na kara dankon zumunci tsakanin iyalai.

Babban magatakardar majalisar dinkin duniya ta Ahlul-baiti (A.S) ya yi nuni da cewa dangane da wajabcin gudanar da tarukan gidaje na jajantawa da ake gudanarwa ya ce: Tarukan majalisan na kara dankon zumunci tsakanin iyalai.


Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Ayatullah "Reza Ramezani" a yammacin ranar Asabar 16 ga watan Disamba 2023 a lokacin da ake gudanar da taron jaje na Raudeh Khaneh a birnin Rasht, inda ya ke nuni da wajabcin gudanar da tarukan gidajen na Raudeh Khaneh Ya ce: waɗannan tarurrukan a duk shekara suna iya zama ƙarfin wajen haɗawa da tara iyalai a lokuta daban-daban.


Wakilin al'ummar Gilan a majalisar kwararrun jagoranci ya yi ishara da cewa, akwai tarihi mai yawa na gudanar da tarukan addu'o'in gida Raudeh Khaneh a Iran kuma ana kokari sosai akan hakan, inda ya bayyana cewa: Domin gudanar da tarukan cikin gida gwargwadon iko kamata ya yi a rika bibiyarsa domin yana da matukar tasiri ga iyalai da unguwanni.


Ya ci gaba da cewa tarukan Raudeh Khaneh na gida na kara dankon zumunci a tsakanin iyalai, sannan suna da matukar amfani da tasiri wajen kara ilimi a kan addini.


Ayatullah Ramezani ya bayyana cewa a yau wasu iyalai suna fama da munanan damuwa da cututtuka inda ya kara da cewa: Falsafar samuwar iyali ita ce mutum ya kai ga kamala a cikinsa.


Wakilin mutanen Gilan a taron masana harkokin shugabanci ya ci gaba da cewa: A kasashen yamma, kasancewar mutane biyu a karkashin rufin daki ko da kuwa ba mace ne da namiji, suna kiransa sa iyali, wanda kuma yanzu sun tsara wannan abun a kasashen Musulunci ma na cewa idan mutum biyu mata ne ko maza ne to za'a kiransu da Iyali ne.


Ya jaddada cewa: Dole ne mu yi kokarin canza wannan ra'ayi da nazari na yamma kuma idan ra'ayin Yan Adamtaka ya yi tasiri a cikin iyali kuma aka kare hakkin juna, za a rage samun bambance-bambance.


Babban magatakardar Majalisar Duniya ta Ahlul-Baiti (AS) ya lura da cewa: ra'ayoyin siyasa da na Yan kasuwa na karya a cikin gida na daga cikin illolin da iyalai ke fama da su.


A karshe Ayatullah Ramezani ya ce: Iyalan gidan sayyidina Ali (AS) da Sayyida Zahra (S) sun kasance cike da taimakon talakawa, marasa son kai da fifita wasunsu akansu.