Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

16 Disamba 2023

19:44:08
1420845

Labarai Cikin Hotuna Na Lullube Hubbaren Razawi Da Bakaken Sitara Domin Juyayin Shahadar Sayyidah Zahra (AS)

An lullube hubbaren Razawi da bakake a daidai lokacin da ake gudanar da zagayowar shahadar Sayyida Zahra (AS).

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti - Abna ya habarta cewa, a daidai lokacin da ake gudanar da zagayowar ranar shahadar Sayyida Zahra (a.s), an kawata farfajiya da harabar haramin Imamur Ridha As da bakaken banoni masu rubuce-rubuce bisa shirye-shiryen makoki na shugabar Duniyoyi guda biyu Biyu.

Tun daga doron hasumiyar zinari, naqarekhaneh, da saqaqhanah, aka kawata su da kayan ado na hubbaren Razawi, duk an lullube su da baqaqen rubuce-rubuce a matsayin alamtawa na juyayin shahadar Sayyida Zahra (AS).

Haramin Razawi mai alfarma ya kwashe kwanaki da dama yana karbar bakuncin maziyarta da makota masu zuwa jajantawa na ranekun shahadar Sayyidah Fatimatuz Zahra'a A's, kuma a gobe kuma za ta karbi bakoncin al'ummar Fatimiyun, wadanda suka zo wannan wuri mai alfarma domin mika ta'aziyya ga Imam Riza (a.s.)