Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Jummaʼa

15 Disamba 2023

11:43:28
1420448

Wasu ‘Yan Sanda Sun Yi Shahada A Wani Harin Ta'addanci A Yankin Sistan Balucistan Iran

Wasu ‘Yan sanda Sun Yi Shahada a wani harin ta’addanci da aka kai a hedkwatar tsaron cikin gida da ke birnin Rask na kasar Iran

Wannan harin ta’addancin ya yi sanadin mutuwa da raunata wasu ‘yan ta’adda, kamar yadda kuma ya shafi wasu ‘yan sanda inda suka samu raunuka tare da yin shahada.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: kakakin rundunar tsaron cikin gida a lardin Sistan da Baluchestan da ke kudu maso gabashin kasar Iran, ya sanar da kai wani hari na matsorata da 'yan ta'adda suka kaddamar kan hedkwatar Jami'an tsaron cikin gidan gwamnatin kasar a birnin Rask a tsakar daren jiya (Alhamis).

Kamar yadda rundunar tsaron cikin gida da ke lardin Sistan da Baluchestan ta nakalto cewa: Wannan harin ta’addancin ya yi sanadin mutuwa da raunata wasu ‘yan ta’adda, haka kuma wasu ‘yan sanda sun samu raunuka tare da yin shahada.

Rahoton ya bayyana cewa: Kwamandan jami'an tsaron cikin gida a lardin Sistan da Baluchestan ya isa wurin da lamarin ya faru, kuma an shawo kan lamarin.

Birnin Rask birni ne da yake kudancin lardin Sistan da Baluchestan, dake kudu maso gabashin kasar Iran.

.................