Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

11 Disamba 2023

10:34:30
1419196

Mutane 6 Sun MutunYayin Da Wasu 10 Suka Jikkata Sakamakon Harin Ta'addancin Da Kungiyar IS Ta Kai A ƙasar Siriya

Wasu ‘yan kasar Syria da dama ne suka yi shahada tare da jikkata su a lardin Al-Raqqa da ke gabashin kasar Syria, sakamakon harin kwantan bauna da ‘yan ta’addar ISIS suka kai musu ta hanyar dasa bam a jikin mutumin da suka yi garkuwa da su tare da kashe shi.

    Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Wasu gungun 'yan ta'addar Daesh sun yi garkuwa da ma'aikatan karkara su 6 a tazarar kilomita 12 daga birnin Madan na lardin Raqqa, inda suka sako 5 daga cikinsu tare da kashe mutum daya. Bayan haka, fararen hula da ke zaune a wannan kauyen tare da wasu mutane 5 da aka sako, sun nemi wanda aka kashe da kuma 'yan ta'addar ISIS.