Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

10 Disamba 2023

06:52:03
1418789

Sakon Ta'aziyyar Shugaban Majalisar Ahlul Baiti (AS) Ta Duniya Ga Ayatollah Wahid Khurasani.

Bayan rasuwar uwargidan Ayatullah Wahid Khurasani, babban sakataren majalisar duniya ta Ahlul Baiti (AS) ya fitar da sakon ta'aziyya.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya kawo maku maganin sakon Ta'aziyyar Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya Ga Matar Ayatullah Wahid Khurasani wanda ya zo kamar haka: 

Sakon ta'aziyyar Ayatullah Riza Ramezani ya zo kamar haka:


بسم الله الرحمن الرحیم

وَبَشِّرِ الصَّابرِینَ الَّذینَ إِذَا أَصَابَتْهُمْ مُصِیبَهٌ قَالُوا إِنَّا لِلَّهِ وَ إِنَّا إِلَیْهِ رَاجِعُونَ

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Kuma ka yi bushãra ga mãsu haƙuri da waɗanda suke idan wata masĩfa ta sãme su, sai su ce: "Lalle ne mũ ga Allah muke, kuma zuwa gare Shi muke komawa."

Babban Marja'i Ayatullah Malam Haj Sheikh Hussein Wahid Khorasani, Allah ya ya tsawaita alherinsa.

Assalamu alaikum Warahamatullahi 

Ina mika ta'aziyyata ga Mai girma da gidan girma maɗaukaki da dukkan 'ya'yan da suka wanzu bisa rasuwar Matar Mai girma Maɗaukaki, wadda ta mika rayuwarta a cikin kwanakin Fatimiyyah.

Ina addu'ar Allah ya jikan marigayiya Jalila Alawiyah, da gafara da daukakar darajoji, tare da rikon tashi tare da Sayyida Saddikatut Tahira, tsira da amincin Allah su tabbata a gare ta. Ga wadanda suka yi saura kuma ina rokon Allah ya ba su hakuri da lada.

Reza Ramezani

Kum Al-Maqdisa - 9/18/1402