Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

9 Disamba 2023

17:16:10
1418587

Ziyara Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya Zuwa Kenya

Matasa Ku San Kanku, Kada Uu Bari Wasu Su Mallake Ku

Muhimmin abin da muka jaddada a Afirka shi ne ku gane kanku tare da yin nazari domin sanin kanku. Ku wani abu ne mai daraja da kima a wurin Allah, kada ka raina kanka domin za ka iya girma.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya kawo maku cigaban bayanin shugaban majalisar Ahlul-Bait AS ta duniya dangane da ziyarar da ya kai kasashen gabashin Afirka da irin nasarorin da aka samu: 

Dangane da haka, bayan nazari da tuntubar juna da yawa, mun yanke shawarar gudanar da taron matasa a Nairobi, babban birnin kasar Kenya. A wannan taro na yini biyu, matasa 123 da suka fito daga kasashe goma na yankin gabashin Afirka sun halarci taron, wanda ya haifar da kafa kungiyar matasan gabashin Afrika. Mun shirya musu horo kamar su ilimin Artificial intelligence, ilimin kafofin watsa labaru da sanin sabbin al'amura da suka wajaba ga matasa kuma sun sami karbuwa sosai.

  A tarurruka daban-daban, mun jaddada cewa ku matasa ku san kanku, kada ku bari wasu su mallake ku, ku tafiyar da lamari da kanku; Kullum muna jaddada cewa "ku zamo masu kafa hanyar kanku". Kun ga cewa tsarin mulki koyaushe yana ƙoƙari ya sanya abubuwan da ake da su su zamo bisa tsarin da yake so; Kamar batun Falasdinu da ke faruwa; Muna cewa Falasdinu ta kasance ta Falasdinawa, don me za a yi wa mutanen wurin gudun hijira a kashe mata da kananan yara. Ya kamata a gudanar da zaben raba gardama a kasar Falasdinu ta yadda gwamnati za ta kasance a hannun Falasdinawa da kansu kuma al'ummar Palastinu za su yanke hukunci kan makomarsu ba daga waje ba.

Mun jaddada a duk tarukan jama'a, na gaba daya da na kebe wajen cewa ku yarda tare da yin imani da kanku. Na ce wa matasan Afirka, ku zuriyar Bilal Habashi ne, kuma kai kaga yadda wannan adabin ya ke da girma gare su. Wasu mutanen ba su nemi mu'ujiza daga Annabi (SAW) ba domin ita kanta maganarsa ta kasance mu'ujiza a gare su. Wasu kuma sun nemi mu’ujiza daga Annabi sannan suka karbi annabcinsa. Haka nan muna da kashi na uku wadanda suke neman uzuri ako da yaushe da kuma ba za su yi imani da shi ba ko da sun ga mu’ujizozi dubu daga Annabi (SAW). Don haka na ce da su, kuna zaune ne a wata nahiya da wasunku suke kamar Bilal na Habasha, wanda bai roki Annabi (SAW) wata mu’ujiza ba, kuma ya dauki maganarsa a matsayin abin da ya dace da yanayinsa da ruhinsa.

Matasan Afirka a shirye suke tsaf don jin gaskiya da ruhiyya; Mun lura da hakan a wajen gudanar da taruka daban-daban kuma mun sami sakamako mai ma'ana. Misali, a karshen taron Nairobi da aka yi tun safe har zuwa yamma, an kafa kungiyar matasan gabashin Afirka. Matasan Afirka ne ke tafiyar da wannan ƙungiyar kuma ya kamata hakan ya kasance mu kawai mu zamo masu ƙarfafawa, taimako da samar da dandamali. Muhimmin abin da muka jaddada a Afirka shi ne ku gane kanku tare da yin nazari domin sanin kanku. Ku wani abu ne mai daraja da kima a wurin Allah, kada ka raina kanka domin za ka iya girma.


Ina ganin a taron matasa da aka yi a Nairobi, mun cimma fiye da yadda ake tsammani, kuma ya samu karbuwa sosai. Wannan ita ce ziyararmu ta farko zuwa Afirka, inda muka ziyarci kasashen Afirka shida da tsibiri daya, amma abin ban sha'awa game da wannan tafiya shi ne shiri da himmar wannan tsatso wajen koyon abu.

Ɗaya daga cikin matsalolin tafiye-tafiye a Afirka ita ce, baya ga tsadar tikitin jirgin sama, filayen jiragen sama masu dakunan jira yan kadan ne; A cikin kasashe fiye da 50 na Afirka, watakila kasashe 4 ko 5 suna da falo, don haka idan muna son yin balaguro daga wannan ƙasa zuwa waccan, wani lokacin sai mu hau jirage biyu, kuma wataƙila an yi jinkirin kusan awa 5 don kai ga na jirgin gaba...