Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

9 Disamba 2023

16:31:19
1418586

Ayatullah Araki: Ginshikai Uku; Asali Da Al'adu Da Ilimi Suna Taka Rawa Wajen Gina Wayewa.

Member a majalisar koli ta majalisar Ahlul-Baiti (AS) ta duniya ya jaddada cewa, masanin kimiyya na hakika kwararre shine ne wanda ba don kansa yake koyon abu ba, sai dai don warware ayyukan wasu da kuma yi wa jama'a hidima. Inds ce: A kan wannan hanya, Ilimomin dan 'adama na iya jagorantar da shiryar da kimiyyar kayan aiki da haifar da zamantakewa.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Ayatullah “Muhsin Araki” mamban majalisar koli ta majalisar duniya ta Ahlul-baiti (A.S) a taron malamai da daliban Kwalejin Usuluddin Qom, ya bayyana alhininsa game da ranekun juyayin Fatimiyyah, in da daga bisani ya taya dalibai murnar zagayowar ranar dalibai, ko shakka babu mafi girman matsayin wayewa shine abubuwa uku: asali, al'adu da ilimi.

Da yake bayyana cewa ilimi sun dace da yin daidai da al'ada, ya kara da cewa: A cikin al'ummomin Ubangiji, dukkan mutane suna jin nauyin abunda ya doru ga junansu, kamar yadda ruwayar Manzon Allah (SAW) yake cewa "dukkan ninku makiyaya ne kuma dukkanninku za'a tambaye ku akan abun da aka ba shi kiwo" Yazo dangane da wannan al'amari.

Wannan member a majalisar koli ta majalisar Ahlul-Baiti (AS) ta duniya ya jaddada cewa, masanin kimiyya na hakika kwararre shi ne wanda ba don kansa yake koyon abu ba, sai dai don warware ayyukan wasu da kuma yi wa jama'a hidima, ya ce: A akan wannan hanya Ilimin bil'adama na iya jagorantar kimiyyar kayan aiki da haifar da zamantakewa.