Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

6 Disamba 2023

06:07:11
1417765

Mataimakin Ministan Yada Labarai na Yemen a wata hira da Abna:

Gwamnatin Sahayoniya Ita Ce Tantagaryar Manufar Mu / Rikici Na Iya Wuce Batun Jiragen Ruwa.

Yankin gabas ta tsakiya ya zamo kamar dai matattarar makamai ne, kuma wani mahaukaci mai suna Netanyahu da wasu kasashe ke goyon bayansa, yana son fasa wannan runbun makaman.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: biyo bayan gagarumin farmakin da sojojin kasar Yamen suke kaiwa kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da kuma kwace jiragen ruwan yahudawan sahyoniya, mataimakin ministan yada labaran kasar Yemen ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Abna. Kamar yadda kuka sani muna cikin guguwar Al-Aqsa kuma tun farkon wannan yakin muke goyon bayan al'ummar Palastinu bisa umarnin jagoran juyin juya halin Yaman mun fadada ayyukan har zuwa teku.

Nasreddin Amer ya kara da cewa: Dole ne mu jaddada cewa tekun Bahar Maliya na da aminci, kuma babu wani hadari ga jiragen ruwa da ke ratsa ta cikin tekun, amma jiragen da aka ayyana a cikin sanarwar sojojin kasar Yemen kuma na sahyoniyawa ne sune aka halalta kamewa ko halakawa.

Dangane da wajabcin dakatar da mamaye Gaza da kuma martanin da kasar Yemen take yi kan wadannan laifuffuka, ya ce: Suna cewa ayyukan Yemen na da hadari, amma muna gaya musu cewa ci gaba da mamaye Gaza yana da hadari. Wannan tsarin mulki na Yahudawa bai fi mu jarumta ba da jajircewa ba, amma mun fi su jarumtaka da dakewa. A lokacin da duniya ba ta tashi tsaye wajen tunkarar mai zalunci ba, ba za mu mutunta mai zalunci ba.

Mataimakin hukumar yada labaran Ansarullah ya ci gaba da cewa: Suna zarginmu da karbar umarni daga kasar Iran, idan kuwa haka ne, to sai in ce Allah ya sanya Iran ta fara yin irin wannan aiki, amma manufarmu guda daya ce kawai, wanda shine tsayar da keta iyaka a kan Gaza, kuma Muna kokarin wajen ganin ya tabbata da kaiwa gareshi.

A karshe "Nasreddin Amer" ya kara da cewa: "Yankin ya zamo kamar rumbun makamai ne, kuma wani mahaukaci mai suna Netanyahu, wanda wasu kasashe ke goyon bayansa, na kokarin fasa wannan da runbun."


................................................