Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

27 Nuwamba 2023

06:07:08
1415174

Dr. Sayyid Ibrahim Raisi A tattaunawarsa da shugaban kasar Turkiyya;

Shugaban Kasar Iran: Amurka ba ta da ikon yin katsalandan da yanke shawara ga mutanen Gaza

Shugaban ya ce al'ummar Gaza ta hanyar Hamas, a matsayinta na halaltacciyar gwamnati bsa doka da ta fito daga kuri'un al'ummar wannan yanki, su keda hakkin yanke shawara kan makomar Gaza, kuma Amurka ba ta da hurumin tsoma baki ko yanke wata shawara a lamarin al'ummar Gaza, kuma duk wani mataki da suka dauka dangane da hakan, to ba zai cimma ga ci ba.

             Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Shugaban Iran Dr. Sayyid Ibrahim Raisi, a wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban kasar Turkiyya Rajabp Dayyip Erdogan a daren jiya Lahadi, ya bayyana dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu a matsayin abokantaka, mai tarihi da kuma kyakkyawar makobta. Ya bayyana haka yana mai la'akari da cewa yana da muhimmanci a karfafa da kyautata alaka da dangantakar dake tsakanin Tehran da Ankara a bangarori daban-daban na siyasa, tattalin arziki da al'adu.

Shugaban ya bayyana kasashen Iran da Turkiyya a matsayin kasashe biyu masu muhimmanci kuma masu tasiri a duniyar musulmi, ya kuma bayyana fatan hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen biyu zai zama abin koyi na mu'amala tsakanin kasashen musulmi.

A wani bangare na wannan tattaunawar ta wayar tarho, Dr. Raisi ya jaddada cewa Amurka ce mai kashe al'ummar Gaza, ya kuma bayyana duk wani tsoma bakin Amurka kan makomar Gaza a matsayin ci gaba da aikata laifukan da kasar nan take yi wa Falasdinawa.

Yayin da yake ishara da irin hadin kai da zura ido da Amurkawa suke da shi wajen aikata munanan laifukan gwamnatin sahyoniyawan da kisan kiyashin da ake yi wa al'ummar Gaza da ake zalunta, shugaban ya jaddada irin wulakanta da kuma tozartar gwamnatin Amurka a idon al'ummar al'ummar kasashe inda ya ce. : Al'ummar Gaza, ta hannun Hamas, tana a matsayin halastacciyar gwamnati, bisa halastacciyar doka, da ta samu daga kuri'un jama'a, wajibi ne wannan yanki ya yanke shawara game da makomar Gaza, kuma Amurkawa ba su da ikon tsoma baki da yanke shawara ga al'ummar Gaza, kuma duk wani mataki da zasu dauka a cikin wannan al'amari ba zai cimmawa ba.

A cikin wannan tattaunawa ta wayar tarho shugaban kasar Turkiyya Rajab Dayyip Erdoğan ya yi ishara da kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasashen Tehran da Ankara, sannan ya jaddada kokarin da ake na daukaka wadannan alakar zuwa ga gata da kebantacciyar alaka.

Ya kuma jaddada shirin kasarsa na gudanar da taron majalisar koli ta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.