Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

25 Nuwamba 2023

05:23:35
1414583

Kididdigar Laifuffukan Ta'addancin Gwamnatin Sahayoniya Bisa Ga Rahoton Ƙungiyar Kare Hakkin Dan Adam Ta Euro-Mediterranean

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Euro-Mediterranean a daren Juma'ar nan data gabata ta sanar da kididdiga ta baya-bayan nan na laifukan da gwamnatin Sahayoniya ta aikata a zirin Gaza bayan da aka tsagaita bude wuta na kwanaki hudu a zirin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya na nakaltomaku daga Kamfanin dillancin labaran IRNA cewa, shima bisa nakaltowo daga shafin sadarwa na yanar gizo na ‘Shahab’ cewa, Falasdinawa 20,31 ne suka yi shahada tun daga farkon hare-haren da ake kai wa Gaza a ranar 7 ga watan Oktoba.

Wannan kungiya ta sanar da cewa 8,176 daga cikinsu yara ne.

Wannan cibiya ta sanar da cewa: Tawagarmu ta buga 'yan mintoci kadan da suka gabata sabbin kididdiga kan adadin Falasdinawa da aka kashe, wanda har da wadanda ke karkashin baraguzan ginin, kuma ba su da damar tsira.

Ita ma wannan kungiyar kare hakkin bil'adama ta bayyana cewa: Mun damu matuka game da rahoton da ke nuni da cewa akwai yuwuwar hukumar lafiya ta duniya ta dauki nauyin yin garkuwa da manyan ma'aikatan asibitin Shafa da cewa da gangan ko kuma ba da gangan ba!.

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Turai da Mediterranean ba ta sanar da karin cikakkun bayanai da kuma adadin wadanda suka jikkata a hare-haren wuce gona da iri da gwamnatin sahyoniya ta kai a zirin Gaza ba.

An gudanar da rahoton na wannan kungiyar kare hakkin bil adama ne bayan tsagaita bude wuta na kwanaki hudu tsakanin gwamnatin sahyoniyawa da kungiyar gwagwarmaya ta Hamas a zirin Gaza da aka fara da karfe 7 na safiyar ranar Juma'a 24 ga watan Disamba a agogon kasar.

Wanda ya kamata ne a aiwatar da wannan tsagaita wuta a ranar Alhamis 23 ga watan Disamba da karfe 10 na safe agogon Gaza, amma saboda batutuwan fasaha da dabaru, an jinkirta ta da kwana daya a ranar Juma'a.

Tun a ranar 7 ga Oktoba, 15 ga watan Mihr, gwagwarmayar Palastinawa, ta mayar da martani ga mamaya da kuma wuce gona da iri da gwamnatin yahudawan sahyoniya suke yi kan al'ummar Gaza da sauran yankunan da ta mamaye. Kamar yadda aka saba, gwamnatin yahudawan sahyoniya ta mayar da martani ga ayyukan mayakan gwagwarmaya ta hanyar yi wa fararen hula kisan kiyashi tare da jefa bama-bamai a wuraren zama. A karshe dai wannan gwamnatin ta amince da gazawar da ta yi wajen kubutar da mutanen da aka kama tare da mika wuya ga gwagwarmaya.