Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

19 Nuwamba 2023

15:32:52
1413083

Ci Gaba Da Bayanan Jagora

Jagora: Kamata Ya Yi Gwamnatocin Musulunci Su Yanke Alakarsu Ta Siyasa Da Gwamnatin Sahyoniyawan A Kalla Na Wani Takaitaccen Lokaci.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi ishara da cewa: Ya kamata al'ummar Turai da Amurka su matsayinsu dangane irin wannan lamari, su kuma nuna ba sa goyon bayan wariyar launin fata.

Wani batu da Ayatullah Khamenei ya ambata game da batutuwan da suke faruwa a Gaza shi ne gazawar soji da aikin sojan gwamnatin sahyoniyawa.

Ya ce: Duk da yawan hare-haren bama-bamai da aka kai a zirin Gaza kawo yanzu gwamnatin yahudawan sahyoniya ta gaza a yunkurinta domin tun da farko sun ce manufarmu ita ce mu ruguza kungiyar Hamas da gwagwarmaya da shafe su a doron kasa, amma bayan fiye da kwanaki 40 da kuma amfani da dukkanin ikon soja, har yanzu ba su iya yin wannan aikin ba .

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya dauki mummunan harin bam din da aka kai wa asibitoci da mata da kananan yara a Gaza a matsayin wata alama ta tsananin fushin da shugabannin yahudawan sahyoniyawan suke da shi game da shan kashin da suka yi, ya kuma kara da cewa: Irin wannan shan kaye da yahudawan sahyoniya suka yi a Gaza lamari ne na hakika. Don haka ci gaba da shiga asibitoci ko gidajen mutane ba nasara ba ce, domin nasara tana nufin cin galaba a kan daya bangaren, wanda gwamnatin yahudawan sahyoniya ba ta iya cimmawa ba har ya zuwa yanzu kuma ba za su iya ba a nan gaba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Khamenei ya jaddada cewa: girman wannan gazawar ya wuce gwamnatin sahyoniyawa, inda ya ke mai cewa: Wannan gazawar tana nufin kuma gazawar Amurka da kasashen yammacin duniya, kuma a halin yanzu duniya baki daya ta fuskanci cewa gwamnatin da ke da cikakkun kayan aikin soji da kayan aiki ta kasa galaba kan abokin hamayyarta wanda ba shi da ko daya daga cikin wadannan kayyakin aikin.

Haka nan kuma ya kara da cewa a kan ayyuka da ayyukan gwamnatocin kasashen musulmi: A bisa dukkan alamu wasu daga cikin gwamnatocin Musulunci sun yi Allah wadai da laifukan da gwamnatin sahyoniya ta yi a tarurrukan jama'a, wasu kuma har yanzu ba su yi ba, amma hakan bai dace ba. Babban aikinsu shi ne su katse muhimman hanyoyin jijiyoyi da ababen rayuwa ga gwamnatin sahyoniya kuma gwamnatocin Musulunci su hana isarwa wannan gwamnati da makamashi da kayayyaki.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: Kamata ya yi gwamnatocin Musulunci su yanke alakarsu ta siyasa da gwamnatin sahyoniyawan a kalla na wani takaitaccen lokaci.

Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Kada al'ummomi su bari a manta da zaluncin da ake yi wa al'ummar Palastinu ta hanyar ci gaba da tarukan su da muzahara.

A karshe ya jaddada cewa: Muna da yakinin Alkawarin Allah kuma muna fata a nan gaba kuma za mu yi aikin da ya hau kanmu.