Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Jummaʼa

10 Nuwamba 2023

18:19:05
1410272

Gwamnatin Yahudawan Ta Kai Hari Kan "ICU" Na Asibitin Al-Quds Da Ke Gaza

Gwamnatin Yahudawan Ta Kai Hari Kan "ICU" Na Asibitin Al-Quds Da Ke Gaza

Majiyoyin labarai sun ba da rahoton harin da yahudawan sahyuniya suka kai a dakin kulawa na musamman a asibitin al-Quds da ke unguwar Tel Al-Hawa a yammacin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Haka nan kuma ana ci gaba da gwabza kazamin fada tsakanin mayakan gwagwarmaya da sojojin mamaya na Isra'ila a kusa da asibitin Shafa da ke birnin Gaza. Sojojin yahudawan sahyoniya suna ta ruwan bama-bamai a wannan yanki.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Qatar ta yi gargadi game da bayyana aniyar haramtacciyar kasar Isra'ila na yin sabbin kisan kiyashi a asibitin Shafa'i na Gaza tare da yin kira ga kasashen duniya da su gaggauta shiga tsakani don kare asibitin Shafa'i da wadanda ke cikinsa.