Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

28 Oktoba 2023

13:22:24
1405857

Bidiyo | Gaza: Wannan shi ne mafi girman da munin hare-hare ta sama da gwamnatin Sahayoniya ta kai

'Yan jaridun da ke yankin sun ba da rahoton yanayin d ake ciki inda suke cewa: Daga cikin hare-haren bama-bamai da aka kai wa Gaza a daren jiya, abu ne mafi muni da karshen hauka da muka gani; Wannan shi ne hari mafi muni da karfi tun farkon harin 7 ga watan Oktoba na yakin.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya bayar da rahoton cewa ‘yan jarida da ke yankin sun ba da rahotonsu tare da bayyana cewa: Duk cikin hare-haren bama-bamai da ake kai wa a zirin Gaza harin daren jiya, shi ne mafi muni da muka taba gani; Shi ne hari mafi karfi tun farkon yakin. Al'ummar Zirin Gaza dai na ganin tashin bama-bamai mafi girma da karfi daga kasa, ruwa da iska tun farkon yakin ranar 7 ga watan Oktoba.

A sa'i daya kuma, majiyoyin yahudawan sun sanar da cewa, sojojin ruwa da na kasa a zirin Gaza kuma mayakan yahudawan sahyoniya da dama suna nan a sararin samaniyar Gaza. Kamfanin dillancin labaran ABNA ya habarto maku bisa nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na NetBlocks cewa, an katse hanyoyin sadarwa na yanar gizo na zirin Gaza gaba daya da kasashen waje, kuma a sa'i daya kuma mayakan gwamnatin yahudawan sahyuniya na ci gaba da kai hare-hare a zirin Gaza, kuma babu wani hoto da ke fitowa daga ciki.