Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

26 Oktoba 2023

14:08:45
1405291

Palasdinawa 6,546 Ne Aka Kashe A Hare-Haren Da Isra’ila Ke Kaiwa Gaza, Ciki Har Da Yara 2,704

Akalla Falasdinawa 6,546 da suka hada da kananan yara 2,704 ne aka kashe tare da jikkata 17,439 a hare-haren da Isra’ila ta kai tun ranar 7 ga watan Oktoba, in ji ma’aikatar lafiya a Gaza da ke karkashin ikon Hamas a ranar Laraba.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Akalla Falasdinawa 6,546 da suka hada da kananan yara 2,704 ne aka kashe yayin da 17,439 suka jikkata a hare-haren da Isra’ila ta kai tun ranar 7 ga watan Oktoba, in ji ma’aikatar lafiya a Gaza da ke karkashin ikon Hamas a ranar Laraba.

Ma'aikatar ta ce a cikin sa'o'i 24 da suka gabata an kashe Falasdinawa 756 da suka hada da kananan yara 344 a hare-haren da Isra'ila ke kaiwa.

Ma'aikatar ta ce "An yi kisan kiyashi a yankin kudancin zirin Gaza." Da yake magana game da tsarin kiwon lafiya, ma'aikatar ta ce hare-haren sun yi nisa ne tare da lalata cibiyoyi 57, kuma an kashe ma'aikatan lafiya 73, kuma motocin daukar marasa lafiya 25 ba su iya gudanar da aiki a yanzu.