Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

26 Oktoba 2023

13:38:04
1405257

Ramukan Kasa Na Gaza; Sun Zamo Babban Abun Tsoron Sojojin Yahudawan Sahyoniya

Ramukan Kasa Na Gaza; Sun Zamo Babban Abun Tsoro Kuma Dodo ga Sojojin Yahudawan Sahyoniya

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Masu lura da al'amura dai na ganin ramukan karkashin kasa na Gaza na daya daga cikin dalilan da suka sa sojojin Isra'ila suka jinkirta kai hare-hare ta kasa kan Gaza. Ramukan da al'ummar Gaza ke amfani da su wajen isar da man fetir da magunguna da kuma domin kare gwagwarmaya daga hare-haren Isra'ila.

Kafar yada labaran Ingila ta Middle East Eye ta rawaito cewa "Isra'ila na shirin cike ramukan Hamas da iskar gas" domin kawar da wannan mummunan mafarki daa take jin tsoronsa.