Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

26 Oktoba 2023

07:07:59
1405131

Indai Ba'a Ɗauki Wani Mataki Ba Aka Hare-haren Isra'ila Kan Gaza Ba Abinda Zai Zo Nan Gaba Zai Iya Fin Na Yanzu Muni

Indai Ba'a Ɗauki Wani Mataki Ba Aka Hare-haren Isra'ila Kan Gaza Ba Abinda Zai Zo Nan Gaba Zai Iya Fin Na Yanzu Muni

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya kawo maku cikakkiyar tattaunawa da yayi da masanin harkokin dokokin kasa da kasa da ke a Najeriya inda ya samu tattaunawa da Dakta Nuradden Muhammad Umar masani akan alakar siyasar kasa da kasa da ke da dokokin kasa da kasa da ke Najeriya in da muka fara tambayarsa dangane asali na fara wannan yaki da kuma dalilansa dama sakamakon da wannan yaki ya haifar.

1- Bisa la'akari da tsamarin yaki da Hamas ta kaiwa yankunan da Israel ta mamaye tare da maida martanin da Israel ta yi akan hakan wanda ya wuce gona da iri tare da sabawa ka'idojin yaki na kasa kasa ya kuke ganin wannan lamari ta fuskancin sakamakon da wannan yaki zai haifar?

Dakta: Mafarin wannan ya ki ya kasance ne daga hare-haren ban mamaki da dakarun Hamas ta kai da jijjifin safiyar ranar bakwai ga wannan wata na Oktoba da mu ke ciki ga wasu daga cikin wuraren da Isra'ila ta mamaye inda wadannan hare-haren suka zamo abun ban mamaki da basu taba tsammanin zai faru ba, domin ba su shirya masa ba, inda dakarun gwagwarmayar a cikin awowin farkon na wannan harin da suka kai da makamai na rokoki sun harba makamai da suka kai dubu biyar a yankunan da Isra'ila ta mamaye na Falasɗinu, sannan wasu dakarun kafa su kai anfani da motoci irin buldoza suka rusa katangar da Isra'ila ta gina wacce ta takatange su mutanen Gaza daga Yahudawa 'yan mamaya 'yan kama wuri zauna da suke zaune a wuraren da gwamnatin Isra'ila ta kwace daga wajen Falasɗinawa ta mallaka masu, wanda a wannan rana daruruwan yahudawan sun rasa rayukansu cikinsu akwai sojojin Isra'ila da dama, wasu kuma dakarun sun dauke su tafi da su a matsayin yin garkuwa da su.

Su ka rike su matsayin sojojin da akai garkuwa da su a wajen yaki kenan. To a zahiri na gaskiya wannan yaƙi yazo da abubuwan ban mamaki da dama kamar yadda mutane suka san irin yanayin tsarin Isra'ila na kai hare-haren wuce gona da iri na zalunci da ta'addanci, to za'a iya cewa abun bai zo da mamaki ba domin hare-haren da take kaiwa ya munana fiye da yadda mai tunani zai iya tunani, tunda ina muka lura shi yaƙi musamman tsakanin dokokin kasa da kasa kamar yadda ka tambaya to akwai wasu jerin mutane da dokar kasa da kasa da ake kiransa da International Humanitarian law yayi maganar cewa idan an zo yaki to dole ne su bangarorin biyun da suke yaƙi ko da tsakanin wata kasa da wata kasa ne ko kuma tsakanin wata kungiyar wata kasa da ta wata kasar ne dole ne su kiyaye wadannan dokoki, daga cikin wadannan dokokin akwai ba za'a kai hari gurin zama da ya ke na Dararen suka ba, sannan za'a kiyaye mutanen da abasu dauke da makamai, za'a kiyaye mata da ƙananan yara da sauransu duka suna nan a wannan kundin na dokokin kasa da kasa. To amma kuma sai muka lura da cewa ita Israela da ta tashi maimakon take tayi yaki da su 'yan gwagwarmaya na Hamas sai ya zamana tafi mai da hankalinta wurin rushe gidajen fararen hula da kai masu munanan hare-hare tare da kashe kananan yara da mata da tsofaffi wanda kai tsaye hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa amma da yake ita shalele ce sannan duniyar ta mu cike take da rashin adalci su manyan kasashe da ake kira da kasashe masu ƙarfin fada aji a duniya wanda kuma su ne kasashen da suke da kujarar dindindin a kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya musamman kasashen Amurka da Birtaniya da Faransa ya zamo duk wani kudirin da za'a kawo ko da ma na ayi Allah wadai ne da baki ga Isra'ila suna katangar shi suna hana wannan kudirin wucewa bisa dogaro da karfin iko da suke da shi na wannan abun da ake cewa Veto power sannan kuma su ka hana a samu yarjejeniyar tsagaita wuta domin a samu a shigar da kayayyakin agaji zuwa ga mutanen Falasɗinu da suka tagayyara, tunda ina zamu iya tunawa kwana biyu bayan fara wannan yaƙi Isra'ila ta katse wa mutanen Falasɗinu wutar lantarki da Ruwa da abinda ya shafi intanet, to dama cen suna cikin kurkuku ne kamar abinda aka kwatanta irin katange su da akai kamar suna wani nau'in kurkuku ne, to kuma a kazo aka ta'azzara abubuwan da wadannan hare-haren sai ya zamana rayuwa ta yi tsanani wato abubuwa sun munana.

To wannan dai na daga cikin abubuwan da muke ganin indai ba wani mataki aka dauka ba abinda zai zo gaba zai iya fin na yanzu ma muni, musamman da yanzu ita Israela take shirin kaddamar da hari ta kasa inda sojojinta za su shige cikin zirin Gaza din, bayan sun gama rugurguje shi ta sama da jiragen yaki to abun zai kara munana gaskiya. Sai dai kuma fatan Allah ya kawo mana sauki abun.

ABNA: Dakta kuna ganin bisa la'akari da rashin maida martani mai tsanani akan Israel shike sawa ta ke ci gaba da wannan barnar ko kuma akwai wani hadafi ko shiri da tasa gaba wanda dama ta riga ta tsara yin hakan bisa goyon bayan Amurka?

Dakta: Dangane kuma da wannan tambayarka ta biyu kan cewar rashin daukar mataki mai tsanani ne ta ke sanya ita Israela ke ci gaba da abinda ta ke, eh to gaskiya zamu iya daukar shi a haka din amma yanzu idan aka ce daukar mataki mai tsanani ya dogara da shin kana nufin cewa wato su samu wasu kasashe da zai kasance sun hada kai da su sun kaiwa ita Israelan farmaki ki kuma kana nufin a dauki batun Isra'ilan a Kaita kaman wato majalisar dinkin duniya babban zauren Majalisar ko kuwa shi kwamitin tsaron Majalisar domin a ladabtar da ita wanda hakan zai iya yiwuwa ga Kaita kotun duniya bisa ga irin laifuffukan yaki da ta tafka!?

Idan wannan abu na biyu kake magana wato na daukar matakin karkashin komar ita majalisar dinkin duniya wannan abu ne gaskiya da nake ganin zayyi wahala saboda ba yau Isra'ila ta fara irin wannan hare-hare na keta haddi da wuce gona da iri ba, amma babu wani matakin da ake dauka akai, asalima yanzu in kana bibiyar lamuran zaka ga cewa su manyan kasashen fadi suke cewa wannan hare-haren wuce gona da irin da Isara'ila ke kaiwa wai yana a matsayin abun da suke kira da self defense ne a yare na masana dokoki waton kamar kariya ne take ba kanta, to wannan wane irin kariya ne za su dauka suke su kashe yaro da baiji bai ci bai ji bai gaji ba da ba ya dauke da komai indai ba tsabar zalunci da danniya da muke fuskanta a wannan duniya ba da ya zama gama gari. Gaskiya wannan shi ne abun da na ke gani dangane da abinda ya shafi wannan yaki da ake yi a halin yanzu tsakanin ita Israela a bangare guda da kuma su dakarun gwagwarmaya na Hamas da sauran dakarun gwagwarmaya da suka shigar ma su a bangare ɗaya.


Masha  Allah Nagode sosai


Mu ma mun gode sosai mu huta lafiya