Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

24 Oktoba 2023

06:54:17
1404463

Ayatullah Ramezani: Makiya Suna Ƙoƙarin Aiwatar Da da Karkacewar Duniyar Kiristanci A Musulunci

Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya ya ce: Dukkan kokarin makiya doru wajen ganin an aiwatar da karkacewar duniyar Kiristanci a cikin Musulunci, misali a addinin Kiristanci sun ta kaitu akan yin abin da suka yi imani da shi, kuma suna karanta Addu'oi Majami'a a duk ranar Lahadi, amma kuma a gefe guda suna aikata dukkan ayyukan da suka saba da imaninsu.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya wanda yayi tafiya zuwa kasar Malawi bisa gayyatar musulmin kasar ya gana da gungun 'yan Sunni na Malawi

A cikin wannan ganawar, Ayatullah Ramezani ya yi ishara da abubuwan da musulmi suka hadu a tsakaninsu inda ya ce: dukkan musulmi 'yan uwan juna ne mun haɗu a kan tauhidi da makoma da qiyama; Haka nan muna da abubuwa da yawa da suka haɗu a cikin hukunce-hukunce kamar Sallah da Azumi da Hajji da umurni da kyakkyawa da hani da mummuna da jihadi.

Malamin ya yi bayani game da rarrabuwar kawuna da a bayan fage a ke haifar da ita tsakanin mazhabobin Musulunci ya kuma bayyana cewa: masu girman kai suna nufin rarrabuwar kasashen musulmi ne a don haka suna son ganin cewa wadannan kasashen musulmi hamsin da bakwai ba su kai ga hadin kai ba. Idan kasashen musulmi suka hadu, to su ne mafi girman karfin tattalin arziki da siyasa.

Babban shugaban Majalisar Duniya ta Ahlul-Baiti (AS) ya ci gaba da cewa: Makiya sun yi niyyar ruguza kasashen musulmi, don haka wajibi ne mu yi taka tsantsan; Dole ne mu kasance muna tattaunawa da matasa don wayar da kan su game da wannan makirci. Makiya suna tsoron hadin kanmu da hadin gwiwarmu.

Ayatullah Ramezani ya dauki aiwatar da Musulunci tare da Shari'a a aikace a matsayin daya daga cikin ayyukan malaman Musulunci da limaman Juma'a da na Khamsu Salawat inda ya ce: Wasu mutane suna neman Musulunci ba tare da aiki ba, kuma suna da yunkurin gabatar da Musulunci ba tare da Shari'a ba, wanda shi ne Musulunci ba tare da aikata abinda ya ke tattare da shi ba. Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Za a zo wani lokaci da sunan Musulunci kadai zai saura, Alkur'ani kuwa kawai rubutunsa ne zai yi saura.” Ma’ana Musulunci, wanda shi ne matsayin tulu mai cike da ruwa zai kasance ya tsiyaye har ƙarshensa, ma'ana babu abin da zai saura na koyarwarsa.

Ya yi ishara da manufofin makiya game da addinin Kirista inda ya ce: Duk kokarin makiya shi ne aiwatar da karkacewar duniyar Kiristanci a Musulunci, misali a addinin Kiristanci sun ta kaitu akan yin abin da suka yi imani da shi, kuma suna karanta Addu'oi Majami'a a duk ranar Lahadi, amma kuma a gefe guda suna aikata dukkan ayyukan da suka saba da imaninsu. Abin baƙin ciki shine, matasansu yanzu sun nisanta kansu daga yin ibada a cikin coci, kuma Ikilisiyar da kanta tana ƙoƙarin halaka kanta ta hanyar yin auren jinsi.

Babban shugaban majalisar duniya ta Ahlul-Baiti (AS) ya ci gaba da cewa: Yanzu haka makiya suna can suna fakewa da nufin aiwatar da irin wannan tsarin na makarantun yamma a makarantun musulmi, sai zamo bayan shekaru 12 na koyan ilimi, sakamakon wannan tsarin ilimi zai zama tsarin sacular. Wajibi ne kuma ya dace a kula da yaranmu, matasa da samari wadanda suke samar da tsatso na gaba.

Ayatullah Ramezani ya jaddada batun tauhidi da imani da addini inda ya ce: Ku yi kokarin sanin addini daidai da gabatar da shi ga matasa domin bayan matakin tauhidi da imani na addini, dole ne mu yi wani abu domin wannan addini ya shiga cikin yanayin rayuwar mutane.

A karshe ya yi ishara da wani hadisi na Imam Husaini (a.s.) ya ce: A wajen wasu mutane, addini kawai a harshe ya ke; Matukar dai ba a cutar da rayuka da dukiyoyin wadannan mutane ba, to zasu tabbata akan da’awar cewa su masu addini ne, amma idan suka ga barna ko wata asara sai su raba hanyarsu da addini. Muna cikin lokacin karshen zamani ne, kuma riko da addini yana da matukar wahala ka kasance domin kamar ka rike wuta a hannu.