Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

22 Oktoba 2023

13:22:30
1403832

Isra'ila Ta Ruguje Masallatai 31 A Hare-haren Da Ta Kai Gaza

Ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza ya sanar da cewa adadin masallatai da Isra'ila ta lalata tun farkon rikicin baya-bayan nan ya kai masallatai 31 sun kuma yiwa majami'u 3 mummunar barna.

Ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza ya sanar da cewa adadin masallatai da Isra'ila ta lalata tun farkon rikicin baya-bayan nan ya kai masallatai 31 sun kuma yiwa majami'u 3 mummunar barna.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: A cewar rahoton na "Al-Jazeera", wannan ofishin ya kara da cewa: Isra'ila ta kai hari kan cibiyoyin hada-hadar jama'a sama da 15 a kasuwa, gidajen cin abinci da gidajen burodi.