Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

21 Oktoba 2023

13:25:20
1403440

Nasihar Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya Ga Masu Wa'azin Addini A Malawi.

Babban Sakatare Janar na Majalisar Duniya ta Ahlul-Baiti (AS) ya jaddada irin karfin da ake da shi a Afirka, inda ya ke cewa da masu wa'azi: ‘Yan Afirka suna da matukar tausasa ne, ku yi kokarin ba su kwarin gwiwar dogaro da kansu; domin duk lokacin da aka samu Mafi dogaro da kai, za'a samu mafi girman ci gaba da haɓaka.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Ayatullah Riza Ramazani, babban sakataren majalisar duniya ta Ahlul-Bait (AS), wanda ya ziyarci kasar Malawi bisa gayyatar 'yan shi'a da musulmin kasar. Ya samu halartar wata ganawa da malaman masu wa'azi na addini a ginin Makaranta da ke wakilcin jami'ar Al-Mustafa ta kasa da kasa da ke Malawi


A cikin wannan taron, babban sakataren Majalisar Ahlul-baiti (AS) ya shawarci malaman masu wa'azin addini da su ci gaba da kammala karatunsu, inda ya ce: wannan ya zama daya daga cikin tsare-tsarenku, kar ku gamsu da takaitawa akan iya abun da kuka karanta. A makarantar Hawza Idan mutum yana son ya zama malamin addini, ya kamata ya fadada iliminsa sosai. Ina zuwa wurin malamina Ayatullah Jawadi Amuli sau daya a mako muna yin ke bantaccen zama na musamman ina kuma amfani da wannan malami mai daraja. Adadin darussa da na iya rikewa baya ga kwasa-kwasan karatun zamani, na yi karatun Hauza na tsawon shekaru 24 (tun 1362) kuma na yi shekara arba’in ina karantarwa a kowace rana kuma ina cikin bincike, kuma an buga littattafaina sama da littattafai 40. Don haka na ce dole ne ku ci gaba da karatunku, idan za ku iya karatu a jami'a, zai yi kyau hakan domin za ku iya ci gaba da koyarwa a jami'o'i a matsayin malaman jami'a.


Ayatullah Ramezani yayin da yake jaddada fadada karatu a fannin kur'ani, Nahj al-Balagha da Sahifa Sajjadiyeh, Ayatullah Ramezani ya kara da cewa: Idan kana da masaniya da harsuna daban-daban kamar Larabci da Farisa, to kana iya karanta da koyon kur'ani mai tsarki, Nahj al- Balaga, Sahifa da kuma darussan hauza a manyan matakai da ake samu akan Intanet ta sararin samaniya. Lokacin da muka shiga sararin samaniya, mun ci karo da batutuwa da ake da shubuha da yawa suna tasowa waɗanda ke buƙatar nazari mai zurfi kuma dole ne mu sami ingantaccen ilimi a wannan fagen.


Yayi la'akari da mahimmancin sanin yanayin fahimtar masu sauraro a harkar isar da sako, ya jaddada cewa: Ku san masu sauraron ku kuma ku yi magana da su gwargwadon fahimtar su da yanayinsu. A cewar wata ruwaya, mutum ya yi magana da mutane gwargwadon hankalinsu; Ga yara ayi masu da yarensu, ga matasa suma ayi masu da yarensu, ga 'yan samari suma ayi masu da yarensu, manya suna ayi masu da yarensu; Kowa yana bukatar ayi masa bayani da yaren sa. Ya kamata ku yi magana da masu sauraronku da harshen hankali bisa la'akari da yanayin da su ke.


Wannan farfesa na manyan matakai na Hauzah ya kara da cewa: A Berlin, akwai wani karamin gari mai suna Potsdam (wani yanki na babban birni na Berlin), inda wasu suka fara wani aiki a kan batun Kur'ani kimanin shekara 15 kuma suna neman su ce kur'ani littafin Larabci ne, kuma annabinsa Balarabe ne, masu sauraronsa suma Larabawa ne. Har ila yau manufarsu ita ce a ɗauka cewa Alkur’ani ba na kowa da kowa ba ne, ba na dukkan bil’adama ba ne, suna so su ce Turawa da Amurkawa ba da su kur’ani ya ke magana ba ne, don haka mu dauki sashen wa'azinsa mu bar sauran sashensa a gefe. Kasafin kudin farko na wannan aiki ya kai Euro miliyan biyar, wanda ita kanta gwamnati ta biya wadannan kudade, a lokacin da shekaru 15 suka cika, ba su samu sakamakon da ake so ba, duk da cewa jami’an wannan cibiya ba musulmi ba ne, wata kila kuma ma suna samun tallafawar wasu al'amuran daga wasu wurare ta bayan fage. Sun yi wani taro a Berlin na yi jawabi na tsawon kwanaki biyu ko uku na yi bayani a wannan taron na ce: Kur'ani yana da harsuna biyu, harshen tattaunawa da magana, da kuma yaren fahimta.


Harshen fahimtar kur'ani harshe ne na hankali da dabi'a, harshen hankali da dabi'a ba na jiya ba ne ba ne kawai ana iya amfani da wannan harshe jiya da yau da gobe. Harshen yanayi da halittar hankali shine harshen mutum, bai san wani harsunan Turai, Amurka ko Afirka ba, Kur'ani na dukkan bil'adama ne. Na yi tunani sosai game da wannan amsar; Wannan ita ce amsar wadancan matsaloli da shubuhohi.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da yawaitar shubuhohi iri-iri a cikin al'ummar yau, Ayatullah Ramezani ya jaddada cewa: Idan shubuha ta bayyana to wajibi ne a shirya tare da bayar da amsar da ta dace ga wannan shubuha din. Daga cikin shubuhohin da suke cewa: “Shin akwai tilastawa ga karabr addini da ya zamo idan wani ya canza addininsa ya yi ridda kenan, idan kuma hukuncinsa ya tabbata kisan kai ne? Idan har akwai ’yanci a yarda da shiga addini, menene laifin canza addinin? Me ya sa Musulunci ya ke fada da hakan? Dole ne mu yi nazari don mu iya amsa irin wannan shubuha da ke yaduwa.


Babban sakataren Majalisar Ahlul-baiti (A.S) ya kara da cewa: horar da masu haddar kur’ani a kasar Malawi abu ne mai kyau, ta yadda duk abin da za ka fada daga baya ya dogara da kur’ani. Ku kasance da ayoyi ga kowane maudu’i, ku yi qoqarin karanta akalla ayoyi 50 da fahimta a kowace rana, ku tashi minti ashirin kafin sallar asuba, ko da kuwa ba ku da halin yin sallah.


Ayatullah Ramezani ya yi tsokaci da dama ga masu wa'azin inda ya ce: Baya ga adadin masu wa'azin ya kamata a tantance masu kokarin yin aiki da wadanda ba sa yin aikin ta yadda za mu samu ingantacciyar hadin gwiwa a fagen gudanar da tarurrukan ilimi ta hanyar sararin samaniya ko kuma a zahiri. Ƙirƙirar Majalisar Masu Wa'azi wani batu ne mai amfani inda za a iya bincika matsalolin wa'azin da sababbin batutuwa a wannan majalisa. Tabbatar da ci gaba a cikin ayyukan yada addini tare da sabon yanayi na duniya domin ayyukanku ya fi tasiri.


A karshe babban sakataren Majalisar Duniya ta Ahlul-Baiti (AS) ya yi jawabi ga masu isar da sakon addini inda ya jaddada irin karfin da ake da shi a nahiyar Afirka inda ya ce: ‘Yan Afirka suna da matukar tausasawar rai, don haka a yi kokarin ba su karfin gwiwa na dogaro da kansu; domin inds duk aka samu girman dogaro da kai to za'a samu mafi girman ci gaba da haɓaka.