Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

19 Oktoba 2023

11:33:25
1402822

Hanyoyin Samun Mafuta Ga Duniyar Musulunci Domin Kaiwa Ga Samun Madafun Iko A Siyasance Daga Kalaman Babban Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (As) Ta Duniya.

Babban Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (As) Ta Duniya ya ce: Idan har dukkanin dukiyar musulmi ta kasance a hannun su kansu musulman kuma ya zamo gwamnatocin Musulunci suna amfani da wadannan dukiyar, to da duniyar musulmi za ta samu karfin siyasa, kuma karfin tattalin arziki zai biyo bayan ikon siyasa, a karshe ba za’a samu wani wanda zai halastawa kansa cin zarafin Alkur'ani da Annabin Musulunci.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (AS) – ABNA --  ya habarta cewa, an gudanar da taron hadin kaI ne tare da halartar Ayatullah Ramezani, Babban Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (As) Ta Duniya ginin mai wakiltar jami'ar Al-Mustafa ta kasa da kasa a Malawi.

A cikin wannan taro, jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Hussein Al-Wandi, Hujjatul-Islam Wal-Muslimin Taqwi, wakilin jami'ar Al-Mustafa ta kasa da kasa, malaman Shi'a da Sunna, gungun mabiya addinin kirista, bangarori daban-daban na mabiya Shi'a na Malawi da daliban jami'ar Al-Mustafa International University sun halarci wannan taro.

A cikin wannan taron, Ayatullah Riza Ramezani ya jaddada cewa wajibi ne dukkanin musulmi su mayar da Manzon Allah (S.A.W) abin koyi sannan ya kara da cewa: A cikin hadisin manzon Allah (saw) ya zo cewa musulmi 'yan uwan ​​juna ne na addini, kuma a kan haka wajibi ne su gane wajibcin da ke kan su na 'yan uwantaka. Don haka a yau ‘yan’uwa musulmi suna da aaiki mai nauyi a kan junansu. Har ila yau, yana cewa a wata ruwayar: “Musulmi kamar jiki ne, idan wani bangare ya yi ciwo, sauran sassan ma za su dauki ciwo ne, kuma za su taimaka wajen rage wannan ciwo da warkar da su.

Ya ci gaba da cewa a yau makiya Musulunci suna kokarin haifar da sabani a tsakanin musulmi, in da ya kara da cewa: Wajibi ne dukkanmu mu tashi tsaye don hana sabani, ta hanyar hadin kai da hadin gwiwa mu kai ga samun karfin iko da ya kamata, domin mu samu iko a siyasance da al'adu da duk wani abu da yake zamowa abun alfahari da daukaka na musulmi a duniya.

Babban sakataren Majalisar Ahlul-baiti (AS) ya kara da cewa: Idan har dukkanin dukiyar musulmi ta kasance a hannun su kansu musulman kuma ya zamo gwamnatocin Musulunci suna amfani da wadannan dukiyar, to da duniyar musulmi za ta samu karfin siyasa, kuma karfin tattalin arziki zai biyo bayan ikon siyasa, a karshe ba za’a samu wani wanda zai halastawa kansa cin zarafin Alkur'ani da Annabin Musulunci.

Ya ce game da cutarwar da sabani yake haifarwa a duniyar Musulunci: Saboda kasancewar bambance-bambance da sabani da makirci na masu girman kai, a cikin gomomi shekaru uku ko hudu da suka wuce, musulmi ne suka fi fuskantar matsalar.

Babban Malamin Hauza ya ce dangane da hadafi da falsafar manufar aiko Annabi: An aiko Manzon Allah (S.A.W) ne domin ya samar da sulhu da zaman lafiya a tsakanin dukkan bil'adama, don haka bai halatta ga wani da sunan Annabi (SAW) ba ya haifar da sabani tsakanin musulmi. Annabi ya kasance a Makka tsawon shekaru 13; Duk da cewa ana gallazawa musulmi da kuntatawa, sai dai Manzon Allah (SAW) bai ba daa izinin yi yaki ba. Mushrikai sun yanke shawarar kashe Annabi (SAW) kuma aka umarci Annabi (SAW) da ya yi hijira, sai ya fara hijira zuwa Madina. Mushrikai masu taurin kai da tsaurin kai sun taho daga Makka zuwa Madina don yakar musulmi inda  Manzon Allah (SAW) shi kuma ya kare kansa.

Ya kara da cewa: An wajabta wa Manzon Allah (S.A.W) zaman lafiya na adalci domin rahama ta watsu a tsakanin mutane, don haka ya fuskanci masu mulkin kama-karya da masu girman kai da azzalumai. Asali ma an aiko Annabi (SAW) ne don yada rahama ga dukkan bil’adama, shi da kan shi ya ce an aiko ni ne domin na zama rahama. Kalaman Amiral-Muminin (AS) masu taushi da ke cikin Nahjul-Balagha. Suna cewa mutane iri biyu ne: "Ko dai 'yan uwanku ne na addini, ko kuma 'yan uwanku aa halitta." Don haka dole ne a kiyaye mutuncin dan Adam. Tun farkon aiken Manzon Allah (S.A.W) ya yi kokarin sulhunta bangarorin biyu da ke cikin sabani da rashin jituwa, tsakanin Aus da Khazraj an yi yaki kusan shekaru 120 suna kashe juna ba tare da dalilin komai ba. Annabi (SAW) ya sanya tare da kulla ‘yan uwantaka tsakanin Aus da Khazraj, da Ansar da Muhajir.

Ayatullah Ramezani ya bayyana cewa, musulmi suna samun rauni sakamakon sabanin ra'ayi, ya kuma kara da cewa: Rauni shi ne sanadin shan kaye a yake-yake. Amirul Muminin (AS) yana cewa dangane da daya daga cikin abubuwan da ke haifar da shan kaye: “Makiya sun hadu a kan karya, amma ku kuma kun rarrabu akan gaskiya, kuma wannan rarrabuwar ta ku da kauracewarku ita ta jawo mana shan kaye.

A wani bangare na jawabin nasa ya yi bayani game da bukatar duniya ta san Annabi (SAW): Idan an san Manzon Allah (SAW) kuma an san shi a duniya, kowa zai bi shi, amma abin takaici makiya sun yi rashin mutunci tare da cin zarafi ga Annabi (SAW).

Ya kara da cewa: Annabi (SAW) ya yi matukar adawa da wariyar launin fata. A zamanin jahiliyya bakaken fata ba su da wani matsayi, amma Manzon Allah (S.A.W) ya sanya wadanda suke bakar fata su zama muharramansa, kuma su zamo cikin sahabban Annabi (SAW) na farko. Bilal bai taba tambayar Annabi (SAW) wata mu’ujiza ba, domin maganarsa ita kantaa mu’ujiza ce. A Musulunci babu bambanci tsakanin Balarabe da wanda ba Balarabe, baki da fari, sai dai a dabi’u na mutum da na Ubangiji. Don haka Annabi (SAW) ya baiwa kowa kwarin gwiwa.

Idan har dukkanin dukiyar musulmi ta kasance a hannun su kansu musulman kuma ya zamo gwamnatocin Musulunci suna amfani da wadannan dukiyar, to da duniyar musulmi za ta samu karfin siyasa, kuma karfin tattalin arziki zai biyo bayan ikon siyasa, a karshe ba za’a samu wani wanda zai halastawa kansa cin zarafin Alkur'ani da Annabin Musulunci.

Babban sakataren Majalisar Ahlul-baiti (AS) ya bayyana cewa, nahiyar Afirka nahiya ce mai wadata da karfinta, ya kuma kara da cewa: 'yan mulkin mallaka ta hanyar wawashe dukiyar wannan nahiyar, ba su bari wannan arzikin ya amfanar da al'ummomin kasashen Nahiyar Afirka ba, ba su yarda al'ummar Afirka ta yi imani da kanta ba. Da a ce Manzon Allah (SAW) yana raye a yau, da ya bai wa kowane dan Afirka wannan sako da ya yi imani da kansa, ya amince da kansa, ku kuma gamsar da kanku cewa za mu iya. Da a ce Annabi (SAW) yana raye a yau, da ya bayar da wannan sakon cewa: kada ku bari wasu su yanke hukunci akan a kanku da abunda ya kamata ku yi, ku yanke qudirinku kanku, domin ku sami hakkinku.

Yayin da yake ishara da rashin tabbatuwar zalunci, ya ce: zalunci ba zai taba tabbata ba, don haka dole ne a fuskanci kowane zalunci. Annabi (SAW) bai yarda da zaluntar mutane ba. Yahudawan sahyoniyawan sun mamaye kasar Falasdinu tare da raba al'ummarta da muhallansu, amma wannan zaluncin ba zai dore ba, kuma wadanda ake zalunta za suyi galaba akan masu zaluntarsu.

Ayatullah Ramezani ya ce game da hanyoyin samun 'yancin kai na tattalin arziki da siyasa: wajibi ne matasa su yi karatu tare da dogaro da kai su zama masana kimiyya, saboda kasa tana girma da ilimi kuma ilimi yana kawo karfi.

Ya ci gaba da cewa: Ya kamata a sanya ilimi a kusa da ruhi da dabi'u, don haka zaluncin da ake yi wa al'umma a yau ya samo asali ne daga fasikanci da rashin rohaniyya. Kimiyya, halayya, rohaniyya da al'adu suna sa ƙasa ta ci gaba.

Babban magatakardar majalisar duniya ta Ahlul Baiti (a.s) ya bayyana cewa, gwargwadon yawan jahilci a cikin al'umma, to zamewa da bata yana yin yawa, ya kuma kara da cewa: Imam Husaini (a.s) ya ba da ransa ne don kada mutane su fda cikin bata, da rashin tabbas, da rudewa. Kuma ya zamo sun samu hanya da makoma na jindadi.

Ya ce game da hanyoyin samun farin ciki da jindadi: Na farko dole ne mu kai ga tsarin tauhidi da tsarin Ubangiji. Na biyu wajibi ne a aiwatar da adalci a cikin al'umma, kuma aiwatar da adalci a cikin al'umma domin ya kasance fata da buri na dukkan annabawan Ubangiji. Allah yana cewa:

»قُلْ إِنَّما أَعِظُكُمْ بِواحِدَةٍ أَنْ تَقُومُوا لِلَّهِ مَثْنى‌ وَ فُرادى‌«

“Ka ce: “Ina maku wa’azi da kadaitaka, domin ku ku koma ga Allah a daidaiku da tagwaye-tagwaye” samun Ceton dan Adam zai samu ne kawai ta hanyar bin wannan ayar. Ko kuma Allah ya ce a wani wurin:

»يا أَيُّهَا الَّذينَ آمَنُوا استَجيبوا لِلَّهِ وَلِلرَّسولِ إِذا دَعاكُم لِما يُحييكُم«

 “Ya ku waxanda suka yi imani ku amsa wa Allah da Manzon Allah, yayinda ya kiraku zuwa ga abunda za ku rayu cikin aminci”. Muminai dole su amsawa Allah Ta’ala da Manzon (SWA) domin su kai ga rayuwa mai inganci ta hakika.