Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

18 Oktoba 2023

20:22:04
1402698

Ayatullah Ramezani: Ruhaniyya Tana Samun Inganci Ne Kawai Tare Da Ubangiji /Addini Yana Gudana A Kowane Fage Na Rayuwa.

Babban shugaban majalisar dinkin Ahlul-baiti (AS) ta duniya ya jaddada yadda malaman addini suke fuskantar gurbacewar al'umma inda ya ce: A yau wasu gurbatattu suna son kiran bil'adama ne zuwa ga ruhiyyah ba tare da Allah ba, alhali kuwa dole ne mu futo na fito da wannan akida, mu tashi mu ce ruhiyyar ma’anawiyya da Allah kadai ta ke samun hakikaninta. Abin takaici, yanzu a Turai da Amurka, an ƙirƙiri ruhaniyya ta karya kusan dubu huɗu.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (AS) - ABNA - Ayatullah "Reza Ramezani" Babban shugaban majalisar Ahlul-baiti (AS) ta duniya wanda ya je wannan kasa bisa gayyatar 'yan Shi'a da Musulman Malawi. A wata ganawa da ya yi da gungun mabiya addinin kirista na kasar Malawi ya bayyana cewa:  yayin da yake bayyana karkacewar al'ummar masu sassaucin ra'ayi, ya bayyana cewa: Daya daga cikin karkatacewar da masu riya 'yancin kai shi ne: suna daukar cin mutuncin annabawan Ubangiji a matsayin 'yanci; A lokacin da nake Majalisar Addinai a birnin Hamburg, sun gaya mana cewa, sun maye gurbin hoton Annabi Isa (AS) da hoton doki, suka mayar da shi tamkar al’ada, alhali kuwa a mahangarmu, wannan shi ne cin mutunci ne ga abubuwa masu tsarki.

Ya ci gaba da cewa: cin mutuncin Annabi Isa da Musa da Ibrahim da Nuhu (amincin Allah ya tabbata a gare su) abu ne da ba za mu yarda da shi ba, kuma ba ma banbance tsakanin annabawa. Sai dai kash yanzu suna kona Al-Qur'ani suna zagin Annabin Musulunci da sanya hakan a matsayin abu mai kyau. Wulakanta abubuwa masu tsarki yana nufin cewa babu wani abu mai tsarki, kuma da zarar an dauki wani abu a matsayin mai tsarki, sai su kai masa hari su kawar da tushensa.

Ayatullah Ramezani ya dauki hakuri da rangwame a shari'a a matsayin karkata na biyu na al'ummar yammacin duniya, kuma ya dauki sakamakon hakan a matsayin kawar da tsarin addini.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da raba addini da siyasa gaba daya a cikin al'ummomin yammacin duniya, babban sakataren majalisar Ahlul-Baiti (AS) ya ce: Hatsarin yana tattare da yadda siyasa ta rabu da addini, kuma gwamnati ta karkace, kuma a halin yanzu suna yunkurin su janyo addini da coci tare da su ya zamo suna goya amsu baya, don haka a cikin coci ake yin auren jinsi.

Ya ci gaba da cewa: Daga karshe kuma an karkatar da iyalai; Mukan ce iyali ya kunshi namiji, mace da ’ya’ya, yayin da suke kiran kowane abu biyu na ma’aurata da suke rayuwa a karkashin rufin daki daya da iyali, ko da kuwa mata biyu ne ko maza biyu ko mutum da dabba ma duk dayane awajensu.

Ayatullah Ramezani ya jaddada arangamar da malaman addini suke yi da karkacewar al'umma yana mai cewa: A yau suna son kiran bil'adama ne zuwa ga rohaniyya ba tare da Allah ba, alhali kuwa ya zama dole mu yaki hakan, mu mun ce rohaniyya yana samun hakikarsa ne tare da Allah kawai; Abin takaici, yanzu a Turai da Amurka, an ƙirƙiri rohaniyya na karya kusan nau’i dubu huɗu.

Babban shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (A.S) ya ce dangane da alakar tsatson samari masu tasowa: bai kamata alakar wannan samarin ta kasance a taron addu’o’in da za a yi a ranar Lahadi a coci kadai ba, sai dai y zamo dole mu amsa tambayoyinsu a cikin fannoni daban-daban na rayuwarsu. Ya kamata a ce wa matasa kada su karkatu ga imani shi kadai; A lokacin da Alkur'ani ya yin da yake magana a kan zamantakewar Musulunci da na 'yan Adam, yana ba da ingancin tabbata akan abubuwa guda biyu ne, daya imani, daya kuma aiki.

Ya na ganin yafi dace a koma ga littafai masu tsarki ya ce: ya dace a gano karkatattun lamurra da aka kirkira da kuma mayar da martani akansu ta hanyar yin amfani da umarnin Littafi Mai Tsarki da Alkur’ani mai girma. Ya kamata mu ci gaba da yin nazarin ayoyin da suka shafi karkacewar al'umma a cikin Kur'ani da Littafi Mai Tsarki.

Ayatullah Ramezani, yayin da yake jaddada batun da wasu ke neman shafe addini ya bayyana cewa: Na yi wata ganawa da shugaban bishop na Orthodox a Jojiya, ya ce da ni ba ka taba fuskantar mayuwacin zamani na tsawon shekaru 70 na gurguzu ba; Ba su yarda da ibada ta kowace hanya ba, sun mayar da masallatai da coci-coci a matsayin rumbun ajiya. Wasu mutane suna ƙoƙari su mayar da addini kamar camfi kuma suna ƙoƙarin yaƙi shi da dukan ƙarfinsu.

  Babban sakataren Majalisar Ahlul-baiti (AS) ya bayyana aikin da ya doru akan malamin addini inda ya ce: Malamin addini ya nemi raya addini da kiyaye shi. Wata kungiya tana son shafi addini, wata kungiya kuma tana son a raunana addini ko takaita shi kuma a dena aiki da hukunce-hukuncensa. Duka ƙungiyoyin biyu suna nufin kada addinai su zama babban abin da ke damun ɗan adam kuma kada su taka wata rawa a rayuwarmu.

Ya ci gaba da cewa: Idan muka yi imani cewa addini yana gudana a kowane fage na rayuwa, ciki har da tunani, imani, halayya, aiki, al'adu, al'umma, siyasa, tattalin arziki da adalci. Wannan ra’ayi da aka ambata shi ne cikakken mahangar ma’auni na addini ta mahangar malaman Musulunci.

A karshe Ayatullah Ramezani ya bayyana cewa: Ina fatan dukkanin addinai za su dauki nauyin akidarsu tare da isar da koyarwar addini ga matasa. Ba wai muna neman mu mayar da duniyar Kiristanci zuwa Musulunci ba, amma kawai muna so mu ce Kirista ya zamo Kirista ne na gaskiya, Musulmi shi ma ya zamo Musulmi ne na gaskiya.

Ganawar Da Babban Sakataren Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya Ya Yi Da Jakadan Vatkan

A wani bangare na ziyarar tasa zuwa Madagaska, Ayatullah Reza Ramezani, babban sakataren majalisar duniya ta Ahlul-Baiti (AS) ya gana da Thomas Grisa, jakadan Vatican a wannan kasa. "Hassan Ali Bakshi" jakadan Iran a Madagascar, da Saeed Jazari shugaban jami'ar Ahlul-Baiti, Hujjatul-Islam Walmusulmi, sun halarci wannan ganawa.

"Thomas Grisa", jakadan fadar Vatican a Madagascar, a wannan taron, yayin da yake magana kan ayyukan masu adawa da addini a duniya, ya ce: "Babban matsalar da muke da ita a duniya a yanzu ita ce batun masu da’awar 'yancin kai wanda ke tafiyar da mulkin" Wannan yunkuri na neman sanya addini a matsayin abin da ya kebanta da al’amuran al’adu, ba wai a matsayin wani lamari da aka kafa da yada shi a cikin al’umma ba. A cikin wannan tsarin, ana bayyana addini a matsayin abin da ya saba wa zamani kuma ba ya barin mutum ya ci gaba ta hanyar zamani. Don haka wannan al’amari yana damun mu duka, ‘yan Shi’a da Katolika.

Ya ci gaba da cewa: Manufar Paparoma game da halin da ake ciki na sassaucin ra'ayi a halin yanzu shi ne cewa mu matsa zuwa ga matakin mutunta kowa da kowa, mu nemi mutunta juna a mataki na farko sannan mu dauki matakai na fannin mutuntuka. Sauran matakan da muka dauka su ne a bahasin ‘yancin addini da akida, ko shakka babu wannan ba yana nufin kowane mutum ya yarda da wani imani da kansa ba, sai dai ya iya gudanar da ibadarsa da raya imaninsa a cikin Muhalli na zamantakewa da kyautatawa kuma ya gabatar da bukuwan farinciinsa wanda ya yarda da su a cikin jama’a, Babban muhimmin bangare na halin yanzu na sassaucin ra'ayi shine wannan ka'ida ta haƙƙoƙin asali.

Jakadan Vatican a Madagaska ya bayyana cewa: Dangantakar mu da 'yan Shi'a ta kara zurfafa bayan ganawar da Paparoma ya yi da Ayatullahi Sistani, kuma ana kokarin fadada wannan kafar dangantakar, a saboda haka ne muka ziyarci cibiyar shi'a ta Khoja, kuma dattawan Shi'a na Khoja za su gana da Paparoma a nan gaba.

A cikin wannan taro, Ayatullah Ramezani, yayin da yake ishara da mamayar da Turawan Yamma suka yi wa addini, ya bayyana cewa: Dabi’un Ubangiji da koyarwar addini da dabi’un dan Adam suna fuskantar babbar barazana a kasashen yammacin duniya, a yammacin duniya muna fuskantar wasu munanan dabi’u da muke gani sun zamo doka ma ta halal. Wajibi ne mu isar da addini ga al'umma bisa ka'idojin wannan zamani da bunkasa lamarin mutuntawa tsakanin mabiya dukkan addinai. Sadarwa da kulla alaka tsakanin shugabannin addini na taka rawa wajen samar da zaman lafiya a duniya.

Ya ci gaba da cewa: Sadarwa da danganta tsakanin shugabannin addini wani nau'i ne na fahimtar iya aiki, kuma tare da daidaito, zai zama nau'in haɗin kai. Dangane da sabbin bukatu da yanayin da muke fuskanta, ya kamata sassan daban-daban su yi nazari mai zurfi dangane da yanayin lokaci da wuri.

Babban Sakatare Majalisar Ahlul-Baiti (AS) ya kara da cewa: Na rubuta wa Paparoma wasiku da dama, daya daga cikinsu na da alaka da lokacin da aka ci mutuncin Manzon Allah (SAW) ya karu da Paparoma, inda na yi masa bayani filla-filla akan bancin da ke tsakanin  'yancin fadin albarkacin baki da cin mutuncin annabawa, ya dauki matsayin yin Allah wadai da wannan cin mutuncin na kuma na yi masa godiya a cikin wasikata tare da jin dadin wannan matsayi kuma ya sake jaddada matsayinsa dangane da wannan wasika.

Hatsarin Wulakanta Abubuwa Masu Tsarki Ga Makomar Addinin Dan Adam

Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin muhimmiyar rawar da malaman addini suke takawa a duniya, Ayatullah Ramezani ya bayyana cewa: Wajibi ne malaman addini su taka rawa a fagen warware matsalolin da al'ummomin kasa da kasa da kuma hana wasu matsaloli irin su talauci da zalunci da karkata. A matsayina na malamin addini wanda yake a fagen kasa da kasa, matsalolin da nake gani d suke fuskantar addinan Ibrahim shi ne duk wani abu mai tsarki sai a sanya shi ya zama marar tsarki, wulakanta abubuwa masu tsarki yana da hadari ga makomar addinin bil'adama, kuma a cikin tattaunawar da na yi na jaddada wannan batu. A cikin mazhabin Shi'a, dukkan annabawa tun daga Adamu har zuwa cikamakonsu Annabi Muhammad (SAWA), ciki har da Annabi Musa da Annabi Isa, da wasu mutane masu tsarki irin su Sayyidah Maryam, tsarkaka ne, kuma an nanata hakan a cikin Alkur'ani cewa Allah ne ya saukar da Attaura da Injila.

 

Ya ci gaba da cewa: A yau an samar da wani dandali na mu'amala tsakanin malaman addini, kuma wannan lamari ne mai farin ciki da ya faru a birnin Najaf kuma Paparoma ya ziyarci Ayatullahi Sistani, kuma muna farin ciki da gudanar da irin wannan tattaunawa. A matsayinsa na daya daga cikin yankuna mafi karfi a duniyar Shi'a, Qum a shirye take don bunkasa tattaunawa tsakanin addinai, kuma wannan ci gaban, kamar yadda na ambata, zai haifar da ci gaban hadin gwiwa. Domin tattaunawa tana da mahimmanci a gare mu duka.