Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

17 Oktoba 2023

17:44:23
1402231

An bude cibiyar Rasulul Azam (SAWA) A Madagascar

An bude cibiyar Rasul Azam tare da halartar baki daga kasashe daban-daban.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta cewa: an bude cibiyar manzon Allah (SAW) a kasar Madagascar tare da halartar baki daga kasashe da mazhabobi daban-daban.

Daga cikin manyan baki na musamman na bude wannan cibiya, akwai Ayatullah Reza Ramezani, babban sakataren majalisar Ahlul-Bait (AS) ta duniya, Hujattual-Islam Walmuslimeen, Sayyid Jawad Shahrashtani, wakilin Ayatullah Sistani, Hujattual-Islam Walmuslimeen, Sayyid Murteza Murteza, menba a majalisar Ahlul Baiti (AS) ta duniya,

"Amin Nasser", shugaban kungiyar Shi'a ta Khawaja a Afirka, "Nader Jafar", manzon musamman na shugaban kungiyar Khaja ta kasa da kasa, "Muhammed Fazil Kadkani" daga Iran, Hujjatul Islam Walmuslimeen "Husain Saulat" daga Tanzaniya "Zuhair Zulfiqar", shugaban 'yan Shi'a na Khawaja Nairobi, Haj Abdul Karim Abu Yusuf da Haj Nasser Jassim Hassan Al-Sayaq daga Kuwait da Haj Mustafa Muhsin Al Lawati daga Oman.

Gudanar da karatun kur'ani, sai rera waken Ya Mahdi tare da halartar yara da jawabai na musamman na daga cikin bangarori daban-daban na bude cibiyar Rasul Azam (AS).

Sheikh "Hanif" manajan cibiyar Rasul Azam (A.S) na kasar Madagascar, a wajen bude wannan cibiya, ya yaba tare da mika godiyarsa ga dukkan wadanda suka taimaka wajen sayen fili da gina wannan cibiya daga kasashe daban-daban.

Hujjatul-Islam Wal-Muslimin, “Murtaza Murtaza”, yayin da yake ishara da wajibcin riko da Alkur’ani da Iyalan Annabi (SAWA), ya ce: “Lokacin da Manzon Allah (SAW) ya karanta Hudubar Ghadeer a lokacin aikin Hajjin bankwana, ya ce wadanda suke wurin su sanar da wadanda ba su halarta ba a wannan Huduba, a lokacin ba mu nan, amma mun samu masaniya ga makaranta da koyarwar Manzon Allah (SAW) don haka ya zamo wajibi mu ci gaba akan wannan tafarki.

Ya ci gaba da cewa: Ayatullahi Sistani ya ce kada mu kira ‘yan Sunna ‘yan’uwa, sai dai ku ce da su ne rayukanmu. Wannan yana ba da fifiko cewa za mu iya cimma burin karshe kawai ta hanyar haɗin kai a tsakaninmu.

A karshen bikin, Ayatullah Ramezani ya mika godiyarsa ga dukkanin maraja'ai da suka yi aikin Tukur wajen yada ilimin Ahlul-baiti (AS) a duniya inda ya ce: Allah ya dora mu akan adalci da kyautatawa, kuma wannan shi ne fatan dukkanin bil'adama. Allah ya aiko da dukkan annabawa domin su tabbatar da adalci a cikin al'umma da kuma daukaka bil'adama, wannan wata babbar cibiya ce, cibiyar da ake dauke da mai sunan Annabi mai girma (SAW), Annabi ne da aka aiko don tabbatar da darajarsa. Ya kamata kowa da kowa ya yi ƙoƙari ya gane dabi'un ɗan adam da na Ubangiji da kuma samun mutunci na gaskiya ta hanyar samun taƙawa.

Babban shugaban Majalisar Ahlul-baiti (A.S) ya ce: Koyarwar Ahlul Baiti (A.S) dukanta mai kyau ce, kuma wadannan koyarwar sun zama tushe abun sha'awa ga duniya yau. A wannan zamani da muke ciki, muna fuskantar rikicin imani, halyya da kuma asali, koyarwar Ahlul-Baiti (AS) za ta iya ba da wannan asali ga dukkan bil'adama. Al'ummar Dan Adam a yau suna kishirwar koyarwar Ahlul Baiti (AS) da kuma ka'idojinsu masu inganci. Abin da ke cikin Alkur'ani da maganganun Ahlul Baiti (a.s) na daya daga cikin ka'idoji masu inganci da dukkan bil'adama ke bukatarsu.