Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

17 Oktoba 2023

17:06:44
1402224

An Gudanar Da Taron Malaman Tabligin Addini A Kasar Madagaska tare da halartar babban sakataren majalisar Ahlul-Bait (AS) Ta Duniya

An gudanar da wani taro na masu Tabligin addini a Madagascar tare da halartar Ayatullah Ramadani.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: an gudanar da taron malamai masu Wa'azin addinin musulunci a kasar Madagaska tare da halartar Ayatullah Reza Ramezani, babban sakataren majalisar Ahlul Baiti (A.S) ta duniya makarantar hauza ta Imam Sadiq (A.S.) A.S.) 

A farkon wannan taro, Dr. Sayyid Saeed Rahimi, shugaba mai Wakiltar Jami'atul Al-Mustafa a Madagaska, ya yaba da ayyukan masu wa’azi na addini a wannan kasa, ya kuma jaddada bukatar karfafar masu wa’azin a kowane fanni.

’Yan’uwa maza da mata masu wa'azi 50 ne suka halarci wannan taron kuma sun gabatar da ra’ayoyinsu game da batun aikin wa’azi a ƙasar Madagascar.

A cikin wannan taro, Ayatullah Ramezani ya ce, yayin da yake ishara da matsayin masu wa'azi: A ranar kiyama za a ce wa kowane daya daga cikin ‘yan wuta cewa mun aiko muku da Nazir, ma’ana gargadi, sai su ce eh an aiko mana da wani Nazir, amma mun ƙaryata shi, da mun ji maganarsa da ba za mu shiga wuta ba. Mai gargadi wani lokacin ta kan kasance Annabi (SAW) ne, wani lokacin kuma Imami Ma’asumi, a yanzu kuma mai gargadin ya zamo shi ne mai wa’azi na addini, a lokacin da ya zamo Manzon Allah (SAW) da Imamai Ma’asumai (AS) ba sa nan, masu wa'azi na addini suna daukar matsayinsu na masu yin gargadi.

Ya ci gaba da cewa: Kowane mai wa'azi yana da ayyuka guda uku, daya shine bayyana tsantsar koyarwar Musuluncin Ahlul-Baiti da yarensa na asali, na biyu kuma shi ne iya amsa tambayoyin da ake tasowa kan batutuwa daban-daban, na uku kuma shi ne ba da amsa ga batutuwa da a ke shakkunsu da suka zama ruwan dare a yau, musamman a cikin kafofin sadarwa na zamani.

Wa'azi yana daya daga cikin alamomin Manzon Allah (SAW) kuma dole ne mai wa'azi ya kasance yana da mu'amala irinta Ahlul-baiti don samun damar yin tasiri akan wasu.

Babban Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya ya yi nuni da cewa: na so in je wani wuri, sai na na fara zuwa wajen Ayatullahi Bahjat, sai na ce da shi ka yi ma ni addu'a, sai ya ce dani na bawa Allah hakkin kulawa da kai, kuma kai ma na baka hakkin kulawa da Ubangiji. Shi yayi min bayani sosai da cewa mutane da yawa suna so su shafe sunan Allah daga cikin zukatan muminai don haka kai ya zama dole ka raya ambaton Allah a cikin zukatansu, hakika wannan shi ne umarnin Manzon Allah (SAW) da yace na bar maku amanar abubuwa guda biyu, littafin Allah da Iyalaina.

A karshen taron, mahalarta taron sun gabatar da addu'ar Faraj na Imam Zaman (AS).

................................