Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

16 Oktoba 2023

18:07:34
1401822

Jami’ar Tehran Ta Karrama Jagora Shaikh Zakzaky Da Digirin Girmamawa

A safiyar ranar Asabar din ne, Shaikh Zakzaky da iyalansa suka gana da Jagoran juyin juya halin Musulunci, Ayatollah Sayyid Khamenie a gidansa da ke birnin Tehran. A yayin da ake da ran Shaikh Zakzaky da tawagarsa za su wuce garin Masshad a ranar Lahadi 15/10/2023, don jinyar da ya kai su.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta bisa nakaltowa daga shafin harka Islamiyya cewa: A yammacin ranar Asabar 29 ga Rabiul Auwal 1445 (14/10/2023), Jami’ar Tehran (Tehran University), da ke Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ta shirya gagarumin biki don karrama Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da Digirin Girmamawa.

Jami’ar, ta bai wa Shaikh Ibraheem Zakzaky Digirin Girmamawan ne a bangaren Ilimin Nazarin Duniya, Zaman Lafiya da Warware Rikici (World Studies: Peace and Conflict Resolution).

Da yake jawabi a wajen taron, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya bayyana cewa, ya sadaukar da wannan shaidar ta Doktora ga daliban Harkar Musulunci a Nijeriya da suke karatu a Iran, da kuma ga al’ummar Nijeriya bakidaya.

A shekarar 2020 ma, wata Jami’a a kasar Iraqi ta taba baiwa Shaikh Zakzaky Digirin Girmamawa, a daidai lokacin da yake tsare a kurkukun Buhari.

Shaikh Ibraheem Zakzaky da matarsa Malama Zeenah sun isa birnin Tehran da ke Jamhuriyar Musulunci ta Iran a ranar Laraba 11/10/2023 da nufin samun damar ganin kwararrun likitoci don duba lafiyarsu daga jinyar da suka shafe shekaru takwas suna fama da, tun bayan harin sojojin Nijeriya a kansu a karshen shekarar 2015.

A safiyar ranar Asabar din ne, Shaikh Zakzaky da iyalansa suka gana da Jagoran juyin juya halin Musulunci, Ayatollah Sayyid Khamenie a gidansa da ke birnin Tehran. A yayin da ake da ran Shaikh Zakzaky da tawagarsa za su wuce garin Masshad a ranar Lahadi 15/10/2023, don jinyar da ya kai su.

Ga wasu daga hotunan da muka samu daga kafafen yada labarai daban-daban na yadda bikin ya gudana: