Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

16 Oktoba 2023

04:17:46
1401548

Babban Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya Ya Ziyarci Rukunin 'Yan Shi'a Na Bohra Da Ke Madagascar

Ayatullah Ramezani ya ziyarci rukunin addini da al'adu na 'yan Shi'ar Bohra Dawudi a Madagascar.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Ayatullah Reza Ramezani, babban Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya wanda ya ziyarci kasar bisa gayyatar ‘yan shi’a da musulmin kasar Madagascar, ya ziyarci wannan rukunin addini da harkokin al'adu na 'yan Shi'a da ke Bohra Dawudi na Madagascar.

Masallacin Juma'a, Masallacin Jami'in salloli biyar, Makarantu a matakai daban-daban da suka hada da ajujuwa, dakin gwaje-gwaje, dakin karatu, cibiyar fadakarwa, dakin cin abinci da gidan malamai da dattijai na daga cikin sassan da babban sakataren majalisar Ahlul-baiti (AS) ya ziyarta a cikin rukunin wurare na Shi'a na Buhra Dawudi na Madagascar.

Bayan kammala wannan ziyara jami'an wannan katafaren wuri, a zantawarsu da suka yi da Ayatullah Ramezani, sun bukaci saukaka tafiyar 'yan Shi'ar Bohra Dawoodi daga Madagaska zuwa Iran don ziyartar wuraren ibada.


Har ila yau, a wannan ganawa an gabatar da jami'ar Ahlul-Baiti, tare da tabo batun yiwuwar shigar da daliban da suka kammala karatu daga makarantun Shi'a na Buhra Dawud zuwa wannan jami'a, ciki har da daliban Shi'a na kasar Madagascar.


Buhra Dawoodi Shi'a Complex na Madagascar rukunin ilimi ne, addini da wurin sauka na dakin kwana wanda ke da sassa daban-daban da suka hada da masallaci, bangaren matakin karatu kuwa a wannan makaranta ya kai har zuwa matakin difloma, gidajen kwana 400 da dakin cin abinci. Fiye da kashi 90 cikin 100 na 'yan Shi'a na Madagascar suna rayuwa ne a wannan rukunin.