Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

15 Oktoba 2023

14:03:50
1401370

Muhimman Bayanan Sayyid Khamene’i A Yayin Ganawarsa Da Shaikh Zakzaky

Daga www.cibiyarwallafa.org Jagoran juyin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Khamene’i ya gana da Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky, matarsa, da ‘ya’yansa a ranar Asabar 14/10/2023 (29 Rabi’ul Auwal 1445).

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul Bayt As - ABNA - ya nakalto maku daga shafin www.cibiyarwallafa.org cewa: A yayin ganawar, Imam Khamene’i, ya bayyana cewa, karfin Musulunci na karuwa a dukkan sassan duniya, duk da kokarin bata shi da makiya ke yi ta hanyar yada karairayi a kansa, da nuna shi a mummunan kama, kuma hakan sakamako ne na kokarin ‘yan gwagwarmaya.

Da yake bayani dangane da yanayin Palasdinu, musamman Gaza, Jagoran ya bayyana cewa: “Daya daga tabbacin bayyanar karfin Musulunci a wannan lokaci, za a iya ganinsa a cikin abin da ke faruwa a Palasdinu.”

Yace: “Abubuwan da suka bayyana a Palasdinu a cikin kwanakin nan, musamman jefa bama-bamai, da shahadantar da mata da yara da mazaje, yana raunata zukatan al’umma.” Ya kara da cewa: “Amma duk da haka, ta wani bangaren al’amarin ya bayyana karfin ikon da Musulunci ke da shi a Palasdinu. Insha Allah, wannan gwagwarmayar da aka fara a Palasdinu zai cigaba har ya kai ga samun cikakken nasarar Palasdinawa.”

Ya kuma bayyana cewa: “Jamhuriyar Musulunci tana kara karfi a kowace rana tun sadda aka samar da ita, kuma za ta cigaba da karfi a nan gaba.”

Yace, motsin Musulunci na karuwa a kullum a dukkan sassan duniya. “A yau, Harkar Musulunci na mamaye dukkan sassan duniya, kamar su Afirka, Asia, Europe (Kasashen Turai) da Kudancin Amurka. Da yardar Allah, nasarar wannan gwagwarmaya zai cigaba da karfafa matuka.”

A yayin ganawar, Jagoran Juyin Musulunci ya bayyana jin dadinsa bisa ganawa da Shaikh Zakzaky da iyalansa, ya kuma jinjina musu cewa: “Ku babban misali ne na wadanda suka dake a fagen jihadi a tafarkin Allah, kuma ina fatan ku cigaba da wannan dakewar.”

Shaikh Zakzaky da matarsa, su ma sun nuna matukar farin cikinsu, a yayin da suka bayyana cewa farin cikin da suka ji ba ya misaltuwa. “Muna fatan cewa, da addu’o’inku, da kokarinku da kuma karfafawarku ga al’ummar Musulmi, Musulunci zai cigaba da mamaye dukkan sassan duniya Insha Allah.” Inji Sayyid Zakzaky. Domin karin bayani dama duba muhimman batutuwa na yau da kullum za ku iya lekaws cikin wannan maganar da ke kasa:

http://www.cibiyarwallafa.org/muhimman-bayanan-sayyid-khamenei-a-yayin-ganawarsa-da-shaikh-zakzaky/


Ga wasu daga hotunan ganawar da muka samu daga shafin khamenei.ir