Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

15 Oktoba 2023

09:48:37
1401317

Rahoto Cikin Hotuna Na Taron Bikin Maulidin Manzon Allah (SAW) A Babban Birnin Kasar Uganda

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, an gudanar da taron bikin maulidin manzon Allah (SAW) a masallacin "Bilal" da ke birnin "Kampala" babban birnin kasar Uganda. Babban mai jawabi na musamman a wannan taro shi ne Ayatullah Riza Ramazani, Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya. Kuma dinbin jama'a mabiya mazhabar Shi'a ne mazauna Kampala suka halarci wannan taron maulidi.