Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

15 Oktoba 2023

06:46:43
1401239

Nasihar Da Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya Ga Ɗaliban Shi'a Na Madagascar.

A ci gaba da gudanar da bukukuwan maulidin Annabin Rahama Muhammad (sawa) a kasashen Afirka Ayatullah Ramazani ya ce, yayin da yake ishara da yanayin neman ilimin addini: A bisa al'ada idan mutum ya kasance mai ladabi da ladubban Ubangiji kuma ya samu siffantuwa da sifofin Ubangiji, to zai samu falala da cancanta har ya zamo an ba shi amanar al'amuran addini. Dole ya zamo koyo da koyarwa da gudanar aiki duka su zamo saboda Allah ne.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (A.S) -ABNA- ya bayar da rahoton cewa, Ayatullah Riza Ramizani, Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya ya ziyarci sassa daban-daban na cibiyar Darul Hikma da ke Madagaska karkashin jagorancin Mr. Reza Ali Hirzhi Cibiyar Darul Hikma tana dauke da bangarori guda biyu makarantar hauza da jami'a. 

Bayan kammala ziyarar, an gudanar da biki tare da halartar Ayatullah Reza Ramezani, babban sakataren majalisar duniya ta Ahlul Baiti (AS) da Hujjatul-Islam Wal-Muslimeen Sayyid Jawad Shahrashtani, wakilin Ayatullah Sistani da Hujjatul-Islam Wal- Muslimeen Sayyed Murteza Murtaza, mamba a majalisar koli ta majalisar duniya ta Ahlul Baiti, suna a matsayin manyan baki na musamman a dakin taro na cibiyar Darul Hikma.

A farkon wannan biki wanda ya samu rakiyar dalibai masu tarin yawa daga cibiyar Darul Hikma, an gabatar da shirin karatun kur'ani mai tsarki tare da halartar fitaccen malamin haddar kur'ani mai girma "Muhammed Ali Eslami", sannan kuma Hujjatul-Islam Wal-Muslimin Sayyid Murteza Murteza da Ayatullah Reza Ramezani sun gabatar da jawabai.

A ci gaba da bikin, Ayatullah Ramezani ya ce, yayin da yake ishara da yanayin neman ilimin addini: A bisa al'ada idan mutum ya kasance mai ladabi da ladubban Ubangiji kuma ya samu siffantuwa da sifofin Ubangiji, to zai samu falala da cancanta har ya zamo an ba shi amanar al'amuran addini. Dole ya zamo koyo da koyarwa da gudanar aiki duka su zamo saboda Allah ne.

Ya ci gaba da cewa: Malaminmu Allamah Jawadi Amuli ya raba ladabi zuwa kashi uku, ya ce ladabi ya kasance tare da kai, wato akan kanka, da kuma ladabi ga sauran mutane wajen mu'amala da su da kuma ladabi tare da Allah. An ce mana idan kana so ka tarbiyyantar da kanka to ka tarbiyyantar da kanka da ladabi, ana tsarkake zuciya ne da ladabi.

Babban Shugaban Majalisar Ahlul Baiti (AS) ya kara da cewa: A bisa la'akari da ayoyin Alkur'ani mai girma, mutum ya kasance yana da zurfin fahimtar addini da tunani kan ayoyin Alkur'ani mai girma. Ya kamata mutum ya mika kansa ga Alkur'ani mai girma don ya ga shin yana rayuwa kamar yadda Alkur'ani ya tsara ko a'a. 

Sayyida Zahra (a.s) a lokacin da ta ke son fadin ya Manzon Allah (SAW) ya kasance sai ta ce: ya kasance halayyar Annabi (SAW) Alkur’ani ne, kuma Manzon Allah (SAW) shi ne wakili kuma shi ne mai misalta Alkur’ani a hakika.

Ya ce: Yana da kyau a kawata wannan Darul Hikma da hikima, wanda kuma aka ba shi hikima, an ba shi alheri mai yawa.

A karshen taron an gudanar da sallar jam'i bisa limancin Ayatullah Ramadani a cibiyar Darul Hikma.