Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

14 Oktoba 2023

13:33:21
1400960

Falasdinu Da Gaza: Su Ne Ke Bayyanar Da Ƙarfin Musulunci

Wajibi Ne Kowa Da Kowa A Duniyar Musulmi Ya Taimaki Al'ummar Palastinu.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya gana da jagoran Harkar Musulunci a Najeriya Shaikh Ibrahim Zakzaky da mai dakinsa a safiyar yau asabar.

Kamfanin dillancin labarai Ahlul Bayt (As) - ABNA - ya habarto maku cewa: Jagoran juyin juya halin Musulunci ya gana da jagoran Harkar Musulunci a Najeriya Shaikh Ibrahim Zakzaky da mai dakinsa a safiyar yau asabar ina a ganawar ta su ya ce: A yau daya daga cikin abubuwan da ke nuni da karfin Musulunci shi ne batutuwan da suke faruwa a Palastinu.

Al’amuran da suke faru a ‘yan kwanakin nan a kasar Falasdinu, musamman hare-haren bama-bamai da shahadar mata da yara da maza, suna cutar da zuciyar bil’adama, amma wani bangare na wadannan al’amura na nuni da irin gagarumin karfin da Musulunci ke da shi a kasar Falasdinu, kuma tare da kulawa da falalar Ubangiji Madaukakin Sarki Allah wannan yunkuri da aka fara a Palastinu zai ci gaba da kai ga samun nasarar Palasdinawa.

Wajibi Ne Kowa Da Kowa A Duniyar Musulmi Ya Taimaki Al'ummar Palastinu.

A yau harkar Musulunci tana ci gaba da yaduwa a sassa daban-daban na duniya kamar Afirka, Asiya, Turai da Arewacin Amurka, kuma da yardar Allah za a ci gaba da samun nasarar wannan yunkuri mai karfi.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce dangane da Sheikh Ibrahim Ya'aqub Alzakzay : Kai misali ne na mujahidi na hakika a tafarkin Allah kuma muna fatan za ka ci gaba da jajircewarka.

Gaisuwa ga Khamenei, Gaisuwa ga Zakzaky