Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Jummaʼa

13 Oktoba 2023

20:38:17
1400746

Ayatullah Ramadani: Allah Ya Aiko Annabi Mai Girma (SAW) Zuwa Ga Dukkanin Al’ummomin Bil’adama

Babban shugaban Majalisar Duniya Ta Ahlul-Baiti (AS) ya bayyana cewa: Allah ya aiko Annabi mai girma (AS) zuwa ga dukkanin al'ummomin bil'adama ne, Annabin rahama ne ga duniya, amma abin bakin ciki a 'yan watannin da suka gabata an samu cin mutuncin Manzon Allah (S) da cin zarafin kur'ani mai girma a wasu kasashen wanda hakan ya cutar da zukatan dukkan musulmi.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (a.s) - ABNA - ya habarta cewa, an gudanar da bukukuwan maulidin manzon Allah (s.a.w) bisa daukar nauyin ƙungiyar Shi'a Isna Ashariyyah ta kasar Tanzania tare da hadin gwiwar makarantar hauza ta Imam Sadik (a.s.) a kasar Tanzania. Yankin "Kikogo" a cikin birnin "Darus Salaam" birni mafi girma a Tanzaniya.


Baki na musamman na wannan biki sun hada da Ayatullah Reza Ramezani, babban shugaban majalisar duniya ta Ahlul-Baiti (AS) da Sheikh Ali Negroku, babban Mufti na kasar Tanzaniya, da malaman addinin Shi'a da Sunna daga larduna daban-daban na Tanzaniya.


A cikin wannan biki kuma an gudanar da taron yaye daliban makarantar Imam Sadik (AS) ta kasar Tanzania.


A cikin jawabin da ya gabatar a wajen wannan biki, Ayatullah Ramadani ya yi ishara da fitattun sifofin Manzon Allah (SAW) inda ya ce: Allah ya aiko Annabi mai girma (SAW) zuwa ga dukkanin al’ummomin bil’adama, Annabi rahama ne ga duniya, amma abin takaici a ‘yan watannin nan an samu gudanar cin zarafi ga Annabi, Akram (SAW) da cin mutuncin Alkur’ani mai girma a wasu kasashe wanda hakan ya bakanta zukatan dukkan Musulmi.


Ya ci gaba da cewa: Cin Zarafin Alkur’ani da Manzon Allah (SAW) cin mutunci ne ga ruhi da mutuntaka da hankali da adalci. Wannan wannan cin mutuncin ba wai iya cin fuska ne ga musulmi da adadinsu ya kai biliyan biyu ba, ko kuma cin mutuncin mabiya addinan duniya da suka kai biliyan hudu ba ne, face cin mutunci ne ga dukkanin bil'adama.


Ya yi nuni da cewa: Wani batu kuma shi ne kan ‘yan uwa dalibai da aka gudanar da bikin yaye su shi ne: Manzon Allah (S.A.W) ya ce ku koyi karatun don Allah, kuma ku koyar da shi don Allah, kuma ku yi aiki domin Allah, domin a rinka ambatonku da girma a duniyar Mulki madaukakiya, To yan uwana dalibai ina cewa gareku ba mu da batu akan iyakar kammala karatun addini domin haka ku kun kammala karatun wani mataki ne kwara daya ne kawai kuma ku sani tafarkin koyon ilimin addini yana da zurfi kuma ami ci gaba ne.