Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Jummaʼa

13 Oktoba 2023

13:32:36
1400672

Ko Da Mun Lalata Gaza Gaba Ɗaya, Mu Ne Muka Yi Asara Tun Farko Wannan Yaƙin.

Wani manazarcin Isra'ila A Wata tattaunawa da tashar 13 ta gidan talabijin na gwamnatin Sahayoniya: Ko da mun lalata Gaza gaba daya, mu ne muka yi asara tun farkon wannan yakin.

Nasarar da muka samu ita ce hadakar shugabancin gwamnati guda biyu (gamayyar gwamnati da kungiyar adawa).

Wasu matasa da dama a Gaza sun yi mana barna tare da kashe dubban mutane da jikkata a hannunmu, sun hana mu tafiye-tafiye, sun rufe filayen jiragen sama da kama Isra’ilawa cikin sauki, suna kutsawa cikin matsuguni kamar wasan na’ura mai kwakwalwa, sun tare tituna. To me ya faru da duk kudaden da aka kashe wa sojoji, me ya sa suke ba su albashi mai tsoka, ina makaman da suka ci gaba, duk da hakan ya kamata Isra’ilawa su zama fursuna a Gaza, wannan abin kunya ne ga sojoji.

Tun da aka kafa Isra'ila har zuwa yau, ba mu ga irin wannan wulakanci da keta iyaka ba, hare-haren makamai masu linzami na kara ta'azzara, kuma adadin mutuwar sojojin na karuwa a kowane lokaci.

Ta yaya suka isa iyakar Asdod da Negev da babura, to ina sojojin Gaza, ina manyan sojojin suke, ta yaya suka kutsa kai da lullubi ba wanda ya sani, ta yaya suka kutsa cikin tsarin tsaro, mu mu ya kamata muji kunya, kashe farar hula Nasara ba ta da yawa. Idan duk duniya tana tare da mu, mun sake gazawa ne Wadannan (masu gwagwarmaya) suna son mutuwa (shahada) kamar yadda muke son rayuwa.