Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Jummaʼa

13 Oktoba 2023

13:27:12
1400671

Mutanen Iran Sun Sake Fitowa Suna Masu Shelanta "Mutuwa Ga Isra'ila" A Duk Faɗin Kasar

Al'ummar musulmin kasar Iran sun yi Allah wadai da laifukan da yahudawan sahyoniyawan suke aikatawa inda suka halarci dukkanin jerin gwanon nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu da ake zalunta da guguwar Al-Aqsa tare da rera taken mutuwa ga Isra'ila da kuma mutuwa ga Amurka. Al'ummar birnin Tehran tare da al'ummar sauran biranen kasar sun halarci gagarumin tattaki a yau Juma'a daga mashigar Nawab da ke kan titin Azadi zuwa jami'ar Tehran, inda ake gudanar da sallar Juma'a.