Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

12 Oktoba 2023

17:04:42
1400501

Ayatullah Ramezani: Batun Palastinu Ya Shafi Dukkanin Ƙasashen Musulmi

Babban Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya ya ce: Wajibi ne mu mai da hankali kan abubuwan da suke faruwa a duniyar musulmi da yadda ake mu'amala da musulmi da kuma abubuwan da suke da tsarki na Musulunci. Batun Falasdinu da zaluncin da ake yi wa musulmin Palastinu yana ya shafi dukkanin duniyar musulmi.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti - ABNA -  ya bayar da rahoton cewa, malaman addinin musulunci daga kasashen gabashin Afirka daban-daban sun hallara a Kampala, babban birnin kasar Uganda, domin gabatar da ra'ayoyinsu kan sabbin hanyoyin bayyana koyarwar Ahlul-Baiti (a).

Babban bako na wannan taro shi ne Ayatullah Reza Ramezani, babban sakataren majalisar duniya ta Ahlul-Baiti (AS).

A cikin wannan taro, Ayatullah Ramezani ya ce, yayin da yake ishara da ayyukan malamai: Wajibi ne mu farfado da ambaton Allah a cikin zukata da tunani, kuma wannan nauyi ne mai girma. Malamai da masu Tabligi sune magada aikin annabci a cikin jagorancin al'umma.

Ya ci gaba da cewa: Zamowa mai Tabligi zamowa malami, da zamawa mai bada tarbiyya na daya daga cikin ayyukan malamin addini da ya kamata ya himmantu wajen sauke aikinsa.

Babban sakataren Majalisar Ahlul-baiti (AS) ya kara da cewa: Dole mai Tabligi ya tarbiyyantar da kansa kafin kowa sannan ya karantar da wasu. Ya kamata ya ƙarfafa hanyoyin salonsa, ƙwarewa da sababbin abubuwa kuma ya koyi sababbin kayan aiki. Wajibi ne masu Tabligi su yi amfani da sabbin kayan aiki don yada addinin musulunci da amsa batutuwa da ake shakku akansu.

Ayatullah Ramezani ya yi ishara da wajibcin kula da lamurran da su ke faruwa a wannan lokaci inda ya ce: Wajibi ne masu Tabligi su kula da bukatu na ilimi da dabi’u da siyasa da al’adu da zamantakewa a cikin mimbari da aiwatar da ka’idoji da sharuddan da suke da shi su yi la’akari da al’amuran yau da kullum, in ba haka ba za a iya samun Mu yi juyayin Ashura, amma mu nuna halin ko-in-kula da zaluncin Yazidawan zamaninmu.

Ya ci gaba da cewa: Ya kamata mu mai da hankali kan abubuwan da suke faruwa a duniyar musulmi da yadda ake mu'amala da musulmi da abubuwa masu tsarki na Musulunci. Batun Palastinu da zaluncin da ake yi wa musulmin Palastinu ya shafi dukkanin duniyar musulmi. Idan ba a yi hattara ba, za su juyar da Musulunci ta yadda ba abin da zai yi saura na akidar addini da al'ada.

Babban Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya  ya kara da cewa: Nahiyar Afirka nahiya ce mai wadata kuma tana da damarmaki sosai, wanda ya kamata a amfanar da al'ummar Afirka da wannan dukiya.

Ya yi nuni da cewa: Dole ne mu yi riko da aiki a kungiyance da hadaka, kungiya tana kawo karfi kuma domin gudanar da hakan akwai bukatar hadin kai kan wannan tafarki.