Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

11 Oktoba 2023

18:23:12
1400033

Dandazon Jama'a Sun Tarbi Dalibin Imam Khumaini (RA) A Filin Jirgin Saman Imam Khumaini RA

Sheikh Zakzaky: Muna Fatan Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Ya Zama Ginshikin Share Fagen Bayyanar Imamul Mahdi (AS) + Hoto Da Bidiyo.

Babban Shugaba Na Harkar Musulunci A Najeriya ya ce Dangane da tarbar da dibbin jama'a suka yi masa a filin jirgin sama na Imam Khumaini: "ba ni da wani abu face godiya dangane da wannan nuna soyayya Na yi matukar farin ciki da ganin yadda wannan yawan jama’a da suka taru a filin jirgin Imam Khumaini suna goyon bayan gwagwarmaya ne.

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA- ya ruwaito a yau Laraba 19 ga watan Mehr 1402 wanda ya yi daidai da 11 ga Oktoba, 2023 “Sheikh Ibrahim Zakzaky” Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya ya isa Iran, inda dubban jama’a suka yi masa gagarumar tarba a Filin jirgin saman Imam Khumaini (RA).

Bisa Rahoton da wakilin ABNA ya aiko mana dangane da halin da ake ciki a filin jirgin saman Imam Khumaini, tun farko an sanar da cewa da karfe 9:30 na safe za a gudanar da bikin tarbar Mujahid Malami Sheikh Ibrahim Zakzaky a babban dakin taro na filin jirgin Imam Khumaini, da dimbin jama’a sun zauna jiran isowarsa a babban tashar jirgin sama tun daga karfe 7 na safe.

Da misalin karfe 9:30 tare da sanarwar cewa Shaikh Zakzaky zai fito ne daga bangaren filin jirgin sama na musamman, jama'ar da suka halarci taron sun bi hanya a wajen filin jirgin, inda suka tsaya daf da bangaren filin jirgin domin yin tarba ta musamman ga babban jarumin Afirka.

Duk da yanayin zafi na wancan lokacin, mutane daga sassa daban-daban na maza da mata, matasa da manya, Iraniyawa da wadanda ba Iraniyawa daga kasashe daban-daban irin su Pakistan, Azarbaijan, Afghanistan, Nigeria da sauran kasashe sun hallara a wajen tarbar tasa.

Bayan an dakata ne sai motar da ke dauke da Shaikh Zakzaky ta tsaya a gaban dimbin jama'a da suka zo tarbarsa, sannan wannan fitaccen malamin ya fito daga cikin motar duk da cewa ba shi da wani karfin yanayi na jiki amma ya fito daga motar ya kuma bayani tare da bayyana irin godiyarsa ga irin nuna soyayyar da mutane suka nuna masa.

A wani takaitaccen jawabi da ya yi, yayin da yake mika godiyarsa ga jama’a da suka yi masa kyakykyawan tarba, Shaikh Zakzaky ya ce: “Dukkanmu mun zo duniya ne don yin wata muhimmiyar jarrabawa, kuma shekaru 8 kenan ina cikin wannan jarrabawa ta Ubangiji. Ina fata bayyanar Mahdi (AS) ya zama karshen dukkan ayyukanmu.

Babban Jagora na Harkar Musulunci a Najeriya ya bayyana cewa ba ni da wani abin da zan yi sai dai in yi godiya dangane da nuna irin wannan soyayya, ya kuma kara da cewa: Ina matukar farin ciki da ganin irin wannan duka taron jama'ar na goyon bayan yunkurin gwagwarmaya kuma sun samu halartar wannan wuri. In sha Allahu Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta iya samar da sauyi a duniya baki daya da suka hada da Amurka da Turai da sauran kasashe, ta yadda za a samar da ginshi da share fage na bayyanar Imam Mahdi (A.S).

Matashi Ibrahim ya kasance asalinsa wani matashi ne daga mazhabar Ahlul Sunna ta Maliki a Najeriya wanda ya yi tafiya zuwa Iran a bikin zagayowar ranar samun nasarar juyin juya halin Musulunci da kuma halartar bukukuwan nasarar juyin juya halin Musulunci.

Bayan ya gana da Imam Khumaini ya zama Shi'a, kuma ya karbi Alkur'ani a matsayin kyauta daga Imam Khumaini. Malam Zakzaky ya fara yada koyarwar addinin Musulunci da mazhabar Ahlul Baiti (a.s) a Najeriya yana mai cewa Imam Khumain Ra ya ce masa "ka je ka kira al'ummar Nigeria zuwa ga Musulunci da wannan Al-Qur'ani" ya fara yunkurin fadakarwa da yada koyarwar Ahlul Bayt As a Najeriya  ya kuma kafa Yunkuri na komawa zuwaga koayarwa hakikain musulunci wanda a yau ya zamo wani muhimmin bangare na musulmi da shi'a a cikin kasar da ta ke mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka.




A halin yanzu dubban miliyoyin mutane sun san mzhabar Ahlul Baiti da gwagwarmaya sakamakon kokari da sadaukarwar Sheikh Ibrahim Zakzaky a Afirka.

A shekara ta 1393 (Yuni 2014) kuma a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan ranar Qudus ta duniya da kuma tattakin da 'yan shi'a na Najeriya suka yi na yin Allah wadai da laifukan gwamnatin sahyoniyawan, sojojin Najeriya karkashin jagorancin 'yan leken asiri na sahyoniyawa sun harbe mutane, galibinsu mata ne da kananan yara, kuma da yawa sun yi shahada a wannan lamari.

Sojojin Najeriya sun yi kokarin kama wasu mutane da kuma kai su wani wuri domin azabtar da su. ’Ya’yan Shaikh Zakzaky guda biyu ma suna cikin wadanda aka kama, an azabtar da su ta yadda ba a iya gane su bayan sun yi shahada. Amma na iya gane su. Shi ma dan Sheikh Ibrahim Zakzaky na uku da sojojin suka harbe shi kuma ya yi shahada a hanyar zuwa asibiti.

 

A shekarar 1394 (Disamba 2015) a harin da sojojin Najeriya suka kai gidan Shaikh Ibrahim Zakzaky, an raunata shi tare da kama shi, sannan ‘ya’yansa maza uku da ‘yar uwarsa sun yi shahada a wannan harin.