Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

10 Oktoba 2023

17:21:51
1399791

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci: Ya Jaddada A Wajen Bikin Yaye Daliban Jami’an Sojin Kasar Cewa:

Guguwar 7 Ga Watan October Shan Kaye Ne Ga Gwamnatin Sahayuniya Da Ba Zata Gyaru Ba

Babban kwamandan dukkan Rundunoni ya ci gaba da cewa: A tarihin wannan zamani babu wata al'ummar musulmi da ta fuskanci kiyayyar zalunci marar tausayawa irin zaluncin da gwamnatin sahyoniya ke wa Falasdinawa ba, kuma ba a samu fuskanci matsin lamba da kawanya da rashi kamar wannan al'ummar ba.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Jagoran juyin juya halin Musulunci kuma kwamandan sojojin kasar a safiyar yau a wajen bikin yaye daliban da suka hada da Hafsan jami'o'in sojojin kasar ya kira wadannan dakaru a matsayin sansanin tsaro da daukaka da kuma masu kare martabar kasa, tare da yin ishara da shan kashi Yahudawa a matsayin abu da "ba zai yuwu a Gyara ba". gwamnatin sahyoniya a yunkurin matasan Palasdinawa da suka yi a baya-bayan nan, ya jaddada cewa, musabbabin wannan mummunar guguwar ita ce ci gaba da cin zarafi da cin mutunci na gwamnatin 'yan mamaya ta bogi a kan al'ummar Palastinu, kuma wannan gwamnati ba za ta iya boye mugunyar fuskarta ta hanyar karya da zaluncin al'ummar Palasdinu ba, don boye harin da take kaiwa Gaza da kisan kiyashin da ta ke yi wa al'ummarta, da dora alhakin bajintar matasan Palastinu da wayo da shirinsu akan wadanda ba Falasdinawa ba.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da abubuwan da ba a taba ganin irinsu ba a baya-bayan nan a kasar Falasdinu, Ayatullah Khamenei ya bayyana matsayin jami'an kasar kan wannan muhimmin lamari na siyasa da soja, yana mai nuni da yadda duniya ke amincewa da gazawar gwamnatin sahyoniyawan a cikin wannan lamari yana mai jaddada cewa: wannan tsarin a bangaren soji da na leken asirin kasa ya sha kayen da ba za a iya gyara shi ba, kuma girgizar kasa ce mai muni da ake ganin ba zai yiwu gwamnatin ‘yan tada kayar baya za ta iya gyara zunzurutun wannan lamari a tsarin mulkinta ko da dukkan taimakon Turawan Yamma ba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa, gwamnatin yahudawan sahyoniya bata zamo gwamnatin sahyoniyawan da ta gabata ba bayan kai Hare-haren ranar Asabar 15 ga watan Mehr, wato ranar bajintar matasan Palastinu, ya kuma kara da cewa: Dalilin wannan babban bala'i shi ne ayyukan sahyoniyawa da kansu ne ya jayo mu su shi; Domin lokacin da kuka wuce iyaka na cin zarafi da zalunci, dole ne ku jira "guguwa".

Haka nan kuma ya lissafta matakin jajircewa da ba da fansar kai ta Mujahiddan Falasdinu suka dauka a matsayin mayar da martani ga laifuffukan ‘yan mamaya na tsawon shekaru da dama da kuma karuwarsa a watannin baya-bayan nan ya kuma kara da cewa: Laifin abin da ya faru a baya-bayan nan shi ne gwamnati mai ci da take mulkin gwamnatin ‘yan ta’adda, wadda ba ta yi nasara bai yi shakkar daukar duk wani mataki na zalunci kan al'ummar Palastinu da ake zalunta ba.

Ayatullah Khamenei kuma yayin da yake ishara da irin mugunyar da mahukuntan mamaya suke da shi ya ce: A tarihin wannan zamani babu wata al'ummar musulmi da ta fuskanci kiyayyar zalunci da muzgunawa na gwamnatin sahyoniyawa Irin Falasdinawa ba sannan ba wata al'umma da ta fuskanci matsin lamba, da kawanya, da karanci ba kamar wannan al'umma." Bugu da kari, Amurka da Ingila ba su goyi bayan wata gwamnati azzaluma ba kamar yadda su ke goyon bayn gwamnatin karya...