Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

10 Oktoba 2023

16:40:16
1399741

Bidiyo| Kalamai Masu Kyau Na Wata 'Yar Isra'ila Game Da Haduwarta Da Mayakan Hamas

Sun zo gidana. Na ce da turanci ina da yara guda biyu, abin da na fara gaya musu kenan. Suka waiwaya sai daya daga cikinsu ya ce da ni da turanci: Kar ki damu, mu musulmi ne ba za mu cutar da ke ba.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, a wata hira da ta yi da tashar talabijin ta 12 ta gwamnatin Sahayoniyya, wata 'yar Isra'ila ta ba da labarin shigar da dakarun gwagwarmayar Palasdinawa cikin gidanta kamar haka.

- Sun zo gidana. Na ce da turanci ina da yara guda biyu, abin da na fara gaya musu kenan. Suka waiwaya sai daya daga cikinsu ya ce da ni da turanci: Kar ki damu, mu musulmi ne ba za mu cutar da ke ba. A gefe guda, na yi matukar mamakin wannan, a daya bangaren kuma, ya rage kunci da na ke ciki, Na zauna da ’ya’yana biyu a kan kujera da daya daga cikin mayakan Hamas ya dauko ta daga dakin cin abinci. Wani mutum dauke da makami ne yana tafiya a dakin da ke kusa da mu, sauran kuma sun kewaye gidan. Daya daga cikinsu ya ga ayaba a kusurwar dakin sai ya tambaye ni: Zan iya cin ayaba, sai na ce eh za ku iya da mamaki (sai macen BaIsra’ila tai dariya).

Ɗan Jarida: Me yaran suka ce?

- Babban yarona ya damu sosai Amma kwatakwata ƙaramin yarona bai damu ba kuma yana wasa da Wayar hannu kuma abin da ya tsorata su kadan shine bindigogin da ke hannunsu. Sunyi magana da larabci. Ɗana ya tambaye ni cewa suna tunanin yadda za su ba da hakuri (dariyar mai rahoto da kuma 'yar Isra'ila). Na gaya wa ɗana abu ne mai wuya. Kusan awa biyu a gidanmu suka yi sannan suka rufe kofar suka fice, haka dai.