Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

10 Oktoba 2023

13:30:33
1399627

Bidiyo| An Gudanar Da Bikin Maulidin Manzon Allah (SAW) A Makarantar Hauza Ta Sayyidah Sukaina (AS) Da Ke Kasar Uganda.

Bidiyo| An Gudanar Da Bikin Maulidin Manzon Allah (SAW) A Makarantar Hauza Ta Sayyidah Sukaina (AS) Da Ke Kasar Uganda.

 Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, A daidai lokacin munasabar haihuwar Manzon Allah (S.A.W) da Imam Ja'afar Sadik (AS) an gudanar da biki na musamman a makaranta da makarantar hauza ta Sayyidah Sukaina (AS) da ke Kampala babban birnin kasar Uganda. Ayatullah Ramazani babban shugaba majalisar Ahlul Baiti (AS) ta duniya wanda ya kasance babban bako na wannan biki ya yaba da irin ayyukan da shugaban wannan cibiya Sheikh Husain Al-Awali yake yi wajen inganta da kuma bayyana koyarwar Ahlul Baiti (AS). Makaranta da makarantar hauza ta Sayyidah Sukainah (AS) a Uganda tana da sassa daban-daban da suka hada da gidajen marayu.