Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

8 Oktoba 2023

07:55:02
1398933

Rahoto Cikin Hotuna Na Gudanar Da Taron Maulidin Manzon Allah (S.A.W) A Kasar Uganda Tare Da Halartar Babban Shugaban Majalisar Ahlul-Bait (AS) Ta Dubiya - 2

Rahoto Cikin Hotuna Na Gudanar Da Taron Maulidin Manzon Allah (S.A.W) A Kasar Uganda Tare Da Halartar Babban Shugaban Majalisar Ahlul-Bait (AS) Ta Dubiya - 2

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, an gudanar da tarukan bukukuwan zagayowar ranar haihuwar Shugaba cikamakon Annabawa Muhammadul Mustafa (AS) a yankin Mayoge na kasar Uganda tare da halartar dinbin al'ummar musulmi. wannan taro ya gudana ne tare al'adun gargajiya da aka saba gudanar da su yayin maulidin fiyayyen halitta (sawa), inda mutane suka gudanar da bukukuwan maulidin manzon rahama (SAW) da wake-wake da kade-kade na gargajiya. Ayatullah Riza Ramizani babban sakataren majalisar Ahlul-baiti (AS) ta dunita ya halarci wannan taron biki a matsayin babban bako kuma an tarbe shi kyakkyawar tarba. A wannan taro bisa jagorancin Ayatullah Riza Ramizani an bude cibiyar ta Az- Zahra tare a hukumance cibiyar da ta ke maida hankali kan ayyukan mata na addini da suka shafi zamantakewa da tattalin arziki. Sannan babban sakataren majalisar Ahlul-Baiti (AS) ya ziyarci kabarin shahidi Abdulkadir wanda ya yi shahada a hannun wahabiyawa, ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan marigayin.