Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

7 Oktoba 2023

17:43:56
1398761

Benjamin Netanyahu ya ce, "Muna cikin wani yanayi na yaki Ne ba cikin wani harin soji ba.

"Vinet": Isra'ilawa Dubu 6 Sun Dawo Daga Sina'a Saboda Yanayin Tsaro

A cewar tashar "Vinet" ta Hebrew, a yau ranar Asabar Isra'ilawa 6,000 ne suka dawo daga Sina'a saboda yanayin tsaro, biyo bayan ci gaba da ta'azzarar lamari tsakanin Falasdinawa da Isra'ilawa.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, hukumar kula da yawan jama’a da hijira ta Isra’ila ya bayar da rahoton cewa, ya zuwa yanzu, kimanin ‘yan Isra’ila dubu 6 ne suka koma Isra’ila ta mashigar Taba.

Wannan dai na zuwa ne bayan da kungiyar Hamas ta sanar da fara kaddamar da Operation Ɗufanul Aqsa, da kuma harba makaman roka kusan 5,000 daga zirin Gaza zuwa cikin Isra'ila a cikin rabin sa'a na farko na farmakin.

A cikin sa'o'i na farko na yakin, an kai wasu hare-hare na musamman da Falasdinawa suka yi, inda suka kutsa kai cikin matsugunan Al-Hafar tare da yin artabu da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila, lamarin da ya yi sanadiyar kisa da raunata wasu da dama daga cikinsu, tare da kame wasu da dama daga cikin mazauna yankunan. .

A gefe guda kuma, sojojin Isra'ila sun sanar da fara aikin soji mai suna "Takobin Karfe", inda suka fara kai farmaki a zirin Gaza.

Kakakin rundunar sojin Isra'ila ya ce, muna fuskantar wani gagarumin farmakin da Falasdinawan suka kai ta ruwa da iska da kuma ta sama, inda kuma muka samu kanmu muna fuskantar tarin makaman roka.

Gidan rediyon Isra'ila ya ce mayakan Hamas sun kama 'yan Isra'ila 35 ya zuwa yanzu, yayin da kafafen yada labaran yahudawan suka ce adadin Isra'ilawan da aka kashe ya zuwa yanzu ya kai 40 sannan adadin wadanda suka jikkata ya kai kusan 800.

Kuma wasu faifan bidiyo sun nuna yadda 'yan Isra'ila suke gudun hijirar jama'a daga mazaunansu.

A nawa bangaren, firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce, "Muna cikin wani yanayi na yaki Ne ba cikin wani harin soji ba.