Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

7 Oktoba 2023

13:02:58
1398614

Hizbullah Labanon: Ayyukan Rundunar "Ɗufanil Aqsa" Wani Sako Ne Ga Kasashe Masu Sasanta Dangataka Da Isra'ila

Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, yayin da take taya murnar nasarar da ta samu a yakin da take yi da gwamnatin yahudawan sahyoniya, ta jaddada cewa wannan aiki sako ne ga kasashen da ke neman sasantawa.

 Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - bisa nakalyowa daga Kamfanin dillancin labaran Irna ya habarta maku cewa, a ranar Asabar din nan ce kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta taya al'ummar Palastinu da kuma Mujahidan musamman ma dakarun Qassam da kuma kungiyar Hamas kan farmakinda " guguwar Al-Aqsa" ta kai ga samun nasara.

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon a cikin wata sanarwa da ta fitar ta jaddada cewa, wannan farmakin da aka samu nasara, wani mataki ne mai girma kan ci gaba da aikata laifuka da hare-haren da gwamnatin sahyoniyawan ke ci gaba da kai wa wurare masu tsarki, tare da sake jaddada batun cewa, muradin al'ummar Palastinu da kuma karfin juriya ne kawai zabin fuskantar makiya Sahayoniyawa.

A cikin wannan bayani an bayyana cewa, wannan aiki sako ne ga kasashen larabawa da na musulmi da kuma al'ummar duniya musamman masu neman sulhu da gwamnatin sahyoniyawa, da kuma jaddada cewa batun Palastinu yana nan a raye kuma ba zai gushe ba. har zuwa cin nasara da Samun yanci.

Hizbullah ta yi nuni da cewa, muna gayyatar al'ummar Larabawa da na Musulunci da kuma al'ummar duniya masu 'yanci da su taimaka wa ayyukan yau da kullum da al'ummar Palastinu da gwagwarmayar ke gabatarwa.

Hizbullah ta jaddada cewa tana bibiyar ci gaban da ake samu a yankunan da aka mamaye sosai kuma tare da himma sosai tare da tuntubar shugabannin gwagwarmayar Palastinawa a ciki da wajenta.

A wani bangare na wannan bayani, an bayyana cewa, ta yi nazari kan abubuwan da ke faruwa da kuma yadda ake gudanar da ayyuka a yankunan da aka mamaye, kuma majalisar ministocin gwamnatin sahyoniyawa ta dauki darasi da abubuwan da suke faruwa a wannan fage.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya habarta cewa, tun daga safiyar yau (Asabar) mayakan gwagwarmayar Palastinawa suka fara kai hare-hare na musamman daga yankin Gaza (kudanci) kan wuraren da yahudawan sahyuniya suka mamaye, aikin da ba shi da kwatankwacinsa a cikin shekaru 75 da suka gabata. Rayuwar ‘yan mamaya na yahudawan sahyoniya ta fada cikin firgici.

A safiyar yau ne aka fara gudanar da ayyukan gaggauwa da sarkakiya na gwagwarmayar Palastinawa a yankunan da aka mamaye daga Gaza, kuma rahotannin da ba na hukuma ba sun bayar da rahoton cewa kungiyoyin gwagwarmaya a yammacin gabar kogin Jordan da ma daukacin yankunan da aka mamaye suna shirin tunkarar yahudawan sahyuniya.

Kame sojojin yahudawan sahyoniya 35 da sanarwar da kungiyar Hamas ta bayar da kuma tabbatar da hakan daga majiyoyin yahudawan sahyoniya a cikin sa'o'i uku na farkon wannan farmakin wasu muhimman al'amura ne na musamman na hare-haren da mayakan Falasdinawan suka yi.