Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

7 Oktoba 2023

09:47:48
1398559

An Gudanar Da Maulidin Manzon Allah (SAW) A Kasar Uganda Tare Halartar Dimbin Musulmai

Ayatullah Riza Ramazani, babban sakataren majalisar duniya ta Ahlul-Baiti (a.s) wanda ya yi tattaki zuwa kasar Uganda a matsayin babban bako domin bikin maulidin manzon Allah (SAW) shi ya zamo babban baki ga Shugaban yankin Ammar Abdulkadir, inda ya samu tarba mai armashi a hukumance. kuma ya samu halartar cikin gagarumin taron jama'ar yankin.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, daga na kasar Uganda, an gudanar da bukukuwan zagayowar ranar haihuwar Sayyidul Khatamil Anbiya'a Muhammad Mustafa (AS) a yankin Mayoge na kasar Uganda tare da halartar al'ummar musulmi.

A wannan biki, wanda ya kasance tare da al'adun gargajiya, mutane sun gudanar da bukukuwan maulidin manzon rahama (SAW) da wake-wake da kade-kade.


Ayatullah Riza Ramazani, babban sakataren majalisar duniya ta Ahlul-Bait (AS) wanda ya kasance babban bako a wannan biki, ya samu tarba a hukumance daga wajen shugaban yankin Ammar Abdulkadir, kuma ya samu halarta a wurin taron jama'ar musulmi na murnar zagayowar ranar haihuwar Ma'aiki (Sawa) mai cike da izza na mutanen yankin. Wannan maraba ta yi tasiri na musamman tare da sautuka da wake-wake da kade-kaden yabo tare da yin salati ga Annnabi Muhammadu da iyalansa tsarkaka.

Ayatullah Ramazani, yayin da yake jawabi ga al'ummar kasar Uganda, ya yaba da kokarin da ake yi a kasar Uganda na yada tsantsar ilimi na addini, ya kuma bayyana cewa: Ladubban Annabci da kuma tsarin rayuwa su ne hasken tafarkinmu.

A cikin wannan biki tare da halartar Ayatullah Ramezani, an bude cibiyar Al-Zahra a hukumance tare da mai da hankali kan ayyukan mata na addini, zamantakewa da tattalin arziki.

Sannan babban sakataren majalisar Ahlul-Baiti (AS) ya halarci kabarin shahidi Abdulkadir wanda ya yi shahada a hannun wahabiyawa, ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan marigayin.

karshen sakon