Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

7 Oktoba 2023

07:03:31
1398506

An Kashe 'Yan Ƙungiyar Al-Shabaab 120 A Wani Farmakin Sojojin Somaliya

A hare-haren da sojojin Somaliya suka kai a tsakiya da kudancin kasar, an kashe 'yan kungiyar ta'adda ta Al-Shabaab 120.

 Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, An kashe 'yan al-Shabaab 120 a wani farmakin da sojoji suka kai a yankin Madag da ke tsakiyar Shabelle da ke kudu maso gabashin Somaliya.

Dawud Uwais Jame, ministan yada labaran Somaliya, ya tabbatar da cewa an kashe mayakan Al-Shabaab 100 da suka hada da wasu shugabannin wannan kungiyar a farmakin da sojoji suka kai a yankin Madag.