Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

5 Oktoba 2023

18:18:26
1398176

Shugaban Jami'ar Ahlul-Baiti (AS) Ya Kai Ziyara Jami'ar Kampala

A yayin da ya ziyarci jami'ar Kampala da ke Uganda, Dr. "Jazari" ya ce: Jami'ar Ahlul-Baiti ta kasa da kasa (AS) za ta shirya don karbar bakuncin malamai da daliban jami'ar Kampala.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, a cikin ziyararsa a nahiyar Afirka, Dr. Saeed Jazari Mamoui, shugaban jami'ar Ahlul Baiti ta kasa da kasa, ya ziyarci jami'ar Kampala dake kasar Uganda.

Game da wannan ziyarar, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na ABNA cewa: An kai ziyarar jami'a guda 5 a birnin Enbate na kasar Uganda; Daya daga cikin ganawar dai har da shugaban jami'ar Kampala, wanda shi ne jakadan Uganda a Iran a baya, kuma yana da masaniya kan al'adun Iran. An ziyarci sauran sashen wannan jami'a guda hudu tare da cibiyar kere-kere da fasaha kuma mun yi zaman tattauna da shuwagabanninsu.

Muna da dammaki masu yawa a wajen hadin gwiwar ilimi na Jami'a, wanda ɗayan bangaren shima ya nuna sha'awarsa da wannan haɗin gwiwa.

A bangarori biyar, watau musayar dalibai, damar karin karatu ga Malamai, fadada kwasa-kwasan jami'a, darussan kimiyya na hadin gwiwa ga daliban Uganda da malaman jami'o'i, wanda tuni mun bada tsokacinmu a rubuce kan wannan yarjejeniya kuma yarda cewa za'a sanya hannu kan yarjejeniya a hukumance.

Daga karshe Jazari ya ce: Jami'ar Ahlul-Baiti ta kasa da kasa (AS) za ta shirya domin karbar malamai da daliban jami'ar Kampala.